Gwamna Samuel Ortom ya ziyarci Buhari

Gwamna Samuel Ortom ya ziyarci Buhari

- A ranar Alhamis ne , 30 ga watan yuni, Gwamnan Jihar Benuwe, Samuel Ortom, ya kai wa shugaban kasa Muhammadu Buhari ziyara fadar Shugaban kasa da ke babban birnin tarayya, Abuja. 

Ya kawo ziyara ne shi ne jim da kadan bayan Gwamnan Jihar Nasarawa, Umar Tanko Al Makura , ya ziyarce shi.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina, ya saki hotunan gwamnan da shugaba buhari a fadar.

Gwamna Samuel Ortom ya ziyarci Buhari
shugaba buhari tare da ortom

A ziyarar da ya kai, gwamna ortom ya ce : “Na zo ne domin tattaunawa da Shugaban kasa game da al'amuran da suka shafi tsaro a Jiha ta, sannan kuma akan maganan tattalin arzikin Jihar, domin ya san halinda muke ciki kuma abinda muke fuskanta. Game da tsaro, abubuwan da ke faruwa na masu garkuwa da mutane, kashe kashe, da sauran su.”

Gwamna Samuel Ortom ya kuma yabi Hukumar hana Almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zaman kasa watau EFFC, da gudanar da bincike kuma damke Kakakin majalisar Jihar Benuwe , Terkimbir Ikyange; Mataimakin sa, James Okefe da shugaban masu rinjaye, Benjamin Adanyi. Ya kara da cewa kada a samu wani togaciya wurin yaki da rashawan da ke gudana a kasar.

Gwamna Samuel Ortom ya ziyarci Buhari
samuel ortom da buhari

Baya ga haka, Gwamna Samuel Ortom ya ce dokan hana Fulani makiyaya kiwo a Jihar Benuwe zai fito ba da dadewa ba.Gwamnan ya fadi hakan ne a babban birnin Jihar, Makurdi,a ranar litinin, 27 ga watan yuji, a karshe wata ganawa da su kayi tare da senatocin mazaban jihar guda 3, David Mark, Barnabas Gemade da George Akume. Game da shi, gwamnatin sa baza ta sallamar da Jihar Benue ga Fulani makiyaya ba duk da hare haren da suke kaiwa a kauyuka.

KU KARANTA : Jami’an tsaro na farin kaya sun cafke yan gidan Yarin Kuje

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel