Jami’an tsaro na farin kaya sun cafke yan gidan Yarin Kuje

Jami’an tsaro na farin kaya sun cafke yan gidan Yarin Kuje

Hukumar tsaro ta farin kaya DSS ta cafke Mutanen nan guda 2 da suka tsere daga gidan Yarin Kuje, Hukumar bata fitar da bayani game da inda aka cafko mutanen ba da kuma halin da suke ciki, labarin yayi matukar faranta ma ma’aikata da Gandirobobin gidan Yarin rai.

Kamar yadda kafar watsa labarai ta yanar gizo wato Sahara reporters ta bayyana Maxwell Ajukwu da Solomon Amodu sun yi amfani da falankin katako ne suka haura katangar gidan kason a daidai lokacin da Musulmai ke bude baki da misalin karfe bakwai na yamma.

Jami’an tsaro na farin kaya sun cafke yan gidan Yarin Kuje
Maxwell da Solomon

Idan ba’a manta ba a daidai lokacin da fursunonin suka gudu, sai labarai suka fara yaduwa cewa wai Shugaban masu karajin yantar da Neja Delta Charles Okah ne ya tsere daga gidan kaso, amma dai Jami’in hurda da jama’a na gidan kason Francis Enobore ya karyata batun.

A cewar jaridar Punch, a ranar da yan fursunan suka tsere, ya kamata akwai wasu gadurobobi dauke da makami guda biyu suna tsare da wajen fursunan, amma basu zo aiki ba a ranar. An samu labarin shugaban fursunan Najeriya reshen babban birnin tarayya Daniel Ehindero ya bada odar a tsare Jami’an su biyu a gidan yarin Kuje. Kazalika Shugaban gidajen yari na Kasa, Ahmed Ja’afaru ya bada umarnin cire shugaban gidan yarin Musa Tanko, kuma ya kafa kwamitin binciken lamarin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel