Dan Ghana ya bace bayan halartar cocin TB Joshua

Dan Ghana ya bace bayan halartar cocin TB Joshua

An nemi wani mutumin Kasar Ghana Dotse Darekey mai shekaru 59 da haihuwa bayan ya zo Najeriya ibada a cocin Fasto TB Joshua da ke Legas, an rasa.

Dan Ghana ya bace bayan halartar cocin TB Joshua

 

 

 

 

 

 

Jaridar THE PUNCH tace mutumin mai suna Dotse ya zo garin Legas ne domin wani taron addu’a da aka gudanar a Cocin SCOAN da ke Ikotun. Dotse dai ma’aikacin wani kamfanin mai ne Accra ta Kasar Ghana, yana da ‘ya ‘ya 3. Har wa yau Jaridar tace Dotse Darekey ya zo Garin Tun 5 ga watan Mayun wannan shekarar, inda ya sauka a wani otel a yankin na Ikotun tare da wani abokin sa mai suna Don Emmanuel.

Don da Dotse dai sun je wajen ibada ne a Cocin SCOAN, bayan sun fito ne aka nemi Dotse aka rasa. Abokin Dotse, Don Emmanuel da yake fada ma Jaridar Punch, abin da ya faru yace shi da ya ga bai ga Dotse ba, sai ya dauka ya koma Kasar ne ta Ghana shi kadai, sai daga baya kuma iyalan shi Mr. Dotsen suka kira sa a waya cewa har yanzu fa basu ga Dotse ba.

Emmanuel Don yake cewa: “Wannan ne zuwa na na-biyu Legas, Ni mabiyin wannan Coci ne na SCOAN a Kasar Ghana. Mun zo garin nan (Tare da Dotse) a Ranar 5 ga watan Mayu, muka kama daki a wani otel, ba a cikin harabar SCOAN muke zama ba. Muna ta zuwa addu’o’i, Ranar Lahadi bayan an tashi daga ibada, cikin cincirindon Jama’a na nemi Dotse na rasa, ko da na koma in kara dubawa ban gan shi ba. Kuma ba ya tare da wayar salula. Ko da sanar da ma’aikatan cocin, sai suka ce mani ba su ga kowa ba, baa bin da SCOAN tun da dama asali ba can muke zaune ba. Na garzaya otel din mu, amma shiru. Sai na karasa wajen ‘Yan sanda a ranar Litinin na kai masu kuka, amma har yau dai ba su kara nema na ba. Kuma bai koma gida ba, domin iyalin sa, sun nemi ni. Haka dai jakadancin Kasar Ghana tana da masaniya game da wannan magana,”

 

Jami’an ‘Yan sanda na Jihar Legas sun tabbatar da wannan labari, haka wani ma’aikacin cocin na SCOAN yace za su tattauna game da maganar a Ranar Juma’a.

Asali: Legit.ng

Online view pixel