Real Madrid zata saka Morata cikin cinikin Hazard na Chelsea

Real Madrid zata saka Morata cikin cinikin Hazard na Chelsea

Jaridar Daily Mirror ta ruwaito cewa kulob din Real madrid na shirin saka dan wasan ta Alvaro Morata cikin cinikin shahararren dan wasan tsakiyar Chelsea Eden Hazard.

Real Madrid zata saka Morata cikin cinikin Hazard na Chelsea
Eden Hazard

Shugaban kulob din na Juventus Beppe Moratta ya shaidawa manema labarai cewa Alvaro Morata zai koma kulob din sa na Real Madrid bayan ya share shekaru 2 tare da su tun 2014. A wani labarin kuma dan wasan na Chelsea kuma dan kasar Belgium Hazard ya bayyana shirin sa na koma Real Madrid da Zinedine Zidane yake horas wa.

Mai karatu zai iya tunawa cewar dan wasan na Chelsea kuma dan shekaru 25 ya sha wahala sosai da rashin tabuka abun-azo-a-gani a kakar wasannin Firimiya da ta gabata inda ya buga wasa sau 25 kacal kuma yaci kwallaye 4 kawai.

A wani labarin kuma jaridar AS ta ruwaito cewa kulob din Real Madrid ya doke kulob din PSG ne wajen kokarin siyan dan wasan na Chelsea wanda ya sha wahala sosai a kakar da ta gabata.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel