Kocin Real-Madrid na neman wani dan wasan Kasar Faransa

Kocin Real-Madrid na neman wani dan wasan Kasar Faransa

Kocin Real-Madrid na neman wani dan wasan Kasar Faransa

– Kocin Kungiyar Kwallon Kafa ta Real-Madrid na son a sayo masa Gwarzon Faransa a Gasar EURO 2016.

– Mai horas da ‘Yan kwallon Real-Madrid din na neman wani dan wasan tsakiya na Leicester.

Kocin Kulob din Real Madrid na Kasar Spain, Zinedine Zidane ya nemi Kulob din ta sayo masa dan wasan kulob din Leicester, zakarun gasar ‘Premier league’ Ngolo Kante. Mai horas da ‘yan wasan na Real-Madrid na so a samu wani mai buga lamba 4 na tsakiya bayan Caseimero, a yanzu haka dai, dan Kasar Brazil dinnan Caseimero, shi kadai ne mai taka lamba 4 a Kungiyar. Ganin haka ne Kocin Real-Madrid din Zinedine Zidane yake neman dan wasa Ngolo Kante na Leicester ta Kasar Ingila.

Kocin Real-Madrid na neman wani dan wasan Kasar Faransa

 

 

 

 

Ngolo Kante dai ya cigaba da burge jama’a a gasar Zakarun Nahiyar Turai ta EURO 2016. Dan wasa Kante yayi matukar kokari a duk wasannin sa 4 da ya buga ma kasar sa ta Faransa. Kocin na Real-Madrid ya dade yana neman dan wasan na Kasar sa, sai dai zai buga da Kungiyar PSG ta Faransa wajen sayen Kante, Kungiyar PSG tun ba yau ba tana neman Ngolo Kante. Kwanakin baya dai Kungiyar Real-Madrid din ta ke kokarin sayan dan wasan tsakiyan Juventus, Paul Pogba. Idan har Real-Madrid tayi nasarar sayen dukkanin su, zai zama akwai ‘yan Kasar Faransa har 3 kenan a Kungiyar ta Real-Madrid, idan aka hada da dan wasan ta na baya wato Raphael Varane. Za a samu ‘yan kwallon Kasar Faransa 3 suna taka leda a Filin Santiago Bernabeau na Birnin Madrid na Kasar Spain karkashin koci Zinedine Zidane, wanda shi ma dan Kasar Faransan ne. Dan wasa Kante Ngolo dai ba zai samu buga wasan su da Kasar Iceland ba da za a kara a ranar Lahadi mai zuwa, sakamakon wani kati da ya sha a baya.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel