Gwamnati ta ba da hutu ranakun Litinin da Talata

Gwamnati ta ba da hutu ranakun Litinin da Talata

-Gwamnatin tarayya ta sanar da Talata 5 da kuma Laraba 6 ga watan Yulu a matsayin ranakun hutu domin bikin sallah

-Ana sa rai musulmin duniya za su kawo karshen azumin da suke yi a wadannan ranaku

-Sanarwar ta nemi ‘yan Najeriya da su ci gaba da marawa shugaba Buhari baya

Gwamnati ta ba da hutu ranakun Litinin da Talata
Babban masallacin juma'a na Kano

 KU KARANTA: Labari da dumi-dumi: Kotu ta yanke hukunci kan karar Buhari

Musulman duniya na yin bikin Sallah a kowacce shekara, bayan kammala azumin watan Ramadana

Laftanar Janar Abdurrahman Dambazau mai ritaya, kuma Minstan kula al’amurran cikin gida ne ya sanar da ranakun hutun a madadin gwamnatin tarayya, a Abuja a ranar Alhamis 30 ga watan Yuni.

KU KARANTA: Musulmai da Kirista suyi ma Shugaba Buhari addua’a

Gwamnati ta shawarci mabiya addinin musulunci da kuma sauran ‘yan Najeriya, da su yada darussan kaunar juna, da zaman lafiya, da kuma adalci, wadanda  suka koya a watan Ramadana, ta hanyar aiki da su a mu’amillar su ta yau da kullum, wanda hakan zai taimakawa ci gaban Najeriya baki daya.

Gwamnati ta ba da hutu ranakun Litinin da Talata

Sanarwar hutun, wacce babban sakataren ma’aikatar ya sa hannu a kai ta ce, Ministan ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su yi amfani da wannan dama su yi tunanin batun zaman lafiya da zaman tare, da cudeni-in-cudeka domin samun kasa mai nagarta.

Ministan, a cewar sanarwar, ya yi wa ‘yan Najeriya fatan yin shagalin bikin Sallah lafiya, da kwanciyar hankali, ya kuma yi kira a gare su da su kara marawa shugaban kasa Muhammadu Buhari baya, a kokarinsa na dora kasar a bisa turba mai dorewa na ingantaccen tsarin siyasa.

 

 

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel