Orji Uzor Kalu na addu’a shaidu su mutu- EFCC

Orji Uzor Kalu na addu’a shaidu su mutu- EFCC

-Lauyan Hukumar EFCC,Rotimi Jacobs,yace ,tsohon gwamnan Jihar Abia na addu’an mutanen da zasu yi shaida akan shi su mutu

-Ya tuhumci tsohon gwamnan da jinkirta gurfanar sa

-Lauyan kanu ta mayar da martani, ya ce jinkirin saboda jiran hukuncin Kotun Koli ne

Hukumar EFCC ta tuhumci tsohon gwamnan Jihar Abiya Orji Uzor Kalu, na sa ran mai shaida akansa ya mutu. Hakan ya faru ne a yau Alhamis,30 ga watan yuni a kotu,yayinda lauyan EFCC,Rotimi Jacobs, ya ce abun tuhuma na neman  hanyoyi iri iri domin jinkirta shari’ar sa.

Orji Uzor Kalu na addu’a shaidu su mutu- EFCC
Orji Uzor Kalu

Ana tuhumtar Orji Uzor Kalu ne da karkata kudade jimillan N5.6biliyan a lokacin da yake Gwamnan Jihar Abia. Alkalin kotun, Annuli Chikere,ya fada wa bangaroran guda biyu su zabi wani ranan da suka gamsu dashi domin sake sabon laale.

Rotimi Jacobs yace: “Na san kana jiran watan Disamba ne,wanda lokaci duka shaidun sun mutu Amma lauyan Orji Uzor Kalu, Chris Uche, bai mai da martani ba,sai dai yayi dariya kawai. Yace shi da sauran lauyoyinsa zasu so a zabi rana bayan hutun Sallah. Amma lauyan EFCC yace kawai a cigaba da gurfanar, yace “ ya mai girma mai shari’a, ina son ka bamu daman cigaba da wannan shari’ar”.

Amma lauyan kalu, Chris Uche, ya ki hakan, yace ai sun zo yau ne saboda da gyaran da EFCC tayi wa tuhuman.  Jacobs yace an kira wannan shari’ar a shekarar 2007,ai an dade. Amma lauyan Kalu yace ai jinkirin saboda jiran hukuncin kotun koli ne. Amma Alkalin ya ce “Za’a dakatar da shari’ar ,idan aka dawo ,za’a a cigaba. Ku sani cewa, idan aka dawo babu wani uzuri kuma,”.

KU KARANTA : Buhari ya yaba ma sojojin Najeriya kan kokarin su

Chikere ya dakatar da sari’ar zuwa ranar 27 ga watan Satumba, abun zargin ya amsa sabuwar tambaya.

Orji Uzor Kalu na gurfana ne a kotu da laifin sata da karkatar da kudi daga manufan sa a lokacin da yak e gwamnan Jihar Abia. Akwai karan laifuffuka 37 akan sa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel