Sai kunyi aman kudaden da kuka sace- EFCC

Sai kunyi aman kudaden da kuka sace- EFCC

-  Hukumar hana al mundahana da yiwa tattalin arzikin Kasa zaman kasa watau EFCC ta na ba barayin gwamnati shawara.

-  Hukumar yaki da rashswan ta ce duk barawon da ta kama sai yayi aman abinda ya sata.

Direktan hulda da jama'a na Hukumar EFCC, Osita Nwaja, ya fadi hakan ne a wata hirar da yayi da Hukumar yada labarai ta kasa watau News Agency of Nigeria (NAN) a ranar laraba , 29 ga watan yuni a Jihar Enugu, kudu maso gabashin Najeriya. Nwaja ya sake jaddada cewa Hukumar yaki da rashswan na shirye cif domin kama duk wanda ke da kashi a gindi, kuma gurfanar da shi a gaban shari'ar.

Sai kunyi aman kudaden da kuka sace- EFCC
efcc

Hukumar EFCC ta ce: “Ku amayo abinda kuka sata. An baku ajiyen kudin mutane kun hadiye kuma kun zo kuna ikirarin kuna da hakkin dan adam. Wannan rashin mutunci ne kuma baku da wani hakkin. Kuma EFCC na maimaitawa, wannan ba daidai ba ne."

Sai mun gurfanar da su a gaban shari'ar. Sai su je su saci biliyoyin nairori kuma su je suyi hayan lauyoyi, a nan muke fuskantar matsala da lauyoyi.  Kwanan nan muka kai wasu kotu, kuma su ka zo kare kan su. Sama da manyan lauyoyi 100 suka zo kare mutum 1.

Yayinda yake bayanin cewa yaki da rashawa aikin kowa ne. Ya ce: “Muna samun labarin barayin da muke wa bincike , yawancin su na zama da talakawa, amma talakawan ba zasu gane su ba saboda sun makanta da su. Sai ka ga kudin da aka bayar domin gina hanyoyi, gina asibitocin kula da masu juna biyu, aika yara makarantu na shiga cikin aljihun mutum daya. Sai kaga mutum shi da iyalinsa , da abokan sa, na facaka da dukiyan yan Najeriya.

KU KARANTA : Wike ga EFCC: Baku da ikon da zaku binciki gwamnati na

Kungiyoyin kare hakkoki da dama na jin dadin yaki da rashswan da wannan gwamnati ke yi, yayinda cibiyar kula da marasa galihu watau Centre for the Vulnerable and the Underprivileged (CENTREP) ta yi kira ga Gwamnatin tarayya da ta wallafa sunayen barayin Gwamnatin.

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel