Soyinka yayi magana kan sake tsara Najeriya

Soyinka yayi magana kan sake tsara Najeriya

-Shehin malami Soyinka ya shiga cikin rukunin masu maganar sake tsarin Najeriya

-Mutumin  da yaci lambar yabo ta Nobel yace ana iya tattauna makomar Najeriya.

Dan Nigeria kuma  shehin malami Wole Soyinka yana mai cewa ya kamata 'yan Najeria su rage karfin da gwamnatin tarayya take dashi.

Soyinka yayi magana kan sake tsara Najeriya
Farfesa Wole Soyinka

A wata hira da yayi da jaridar the Punch, Mr. Soyinka yana mai ra'ayin cewa tattara karfin iko da akayi ga gwamnatin tarayya shine musabbabin bacin rai tsakanin jihohin da suka taru sukayi kasar.Ya kamanta yanayin da cin fuska, ya kuma ce hakan shi ke hana gasa mai ma'ana tsakanin jihohin.

Ya ci gaba da cewa "bai dace ba mu bar wannan tattara karfin iko ga gwamnatin tarayya ya ci gaba ba domin yana kawo rashin jituwa tsakanin jihohi. Cin fuska ne a tattara kudaden shiga wuri daya, sai dai kawai a rika 'yamma jihohi, wannan yana hana gasa mai kawo ci gaba tsakanin jihohin, kuma yana hana jihohin hanyar dogaro da kansu.

Ina cikin masu cewa dole ne mu tabbatar da mun kauce ma dargajewa a matsayin kasa daya. Na amince ma wannan maganar, abinda ban gane ba shine maganganun da tsohon shugaba Obasanjo da shugaba Buhari, da magabatansu ke cewa ba za'a iya tattauna kasancewar kasar guda daya ba. Dole mu rika tattauna maganar zamantakewarmu da junammu a kullum".

KU KARANTA : Biyafara ba za ta yiwu ba – APC

Marubucin yayi tsokaci kan shirin da ake na samar ma Fulani makiyaya burtaloli, yana mai cewa mamadin haka, kamata yayi a tanadi wuraren da za'a rika sayar da dabbobi domin kasuwanci.

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel