Sarki Sanusi ya taya sabon Sifeto murna,ya bashi shawara

Sarki Sanusi ya taya sabon Sifeto murna,ya bashi shawara

-Sarkin Kano, Sanusi Lamido Sanusi II, ya taya sabon hafsan sifeton yan sanda,Ibrahim idris, murna.

-Sarki Sanusi yace yanada yakinin sabon sifeton zai gudanar da aikin sa yadda ya kamata.

Sarki Sanusi ya taya sabon Sifeto murna,ya bashi shawara
Sarki Muhammad Sanusi ta biyu na jihar Kano

Sarkin masarautar Kano, Sanusi Lamido Sanusi(muhammadu) II, ya aika sakon taya murna zuwa ga sabon Sifeton yan sanda Ibrahim Idris,akan sabon mukamin da Allah ya bashi. A wasikar taya murnar, sarki sanusi lamido sanusi ya bege sabon sifeton da ya karfafa tabbatar da tsaro a kasar. Jaridar PM ta bada rahoto

Sarkin sanusi lamido sanusi yace duk da cewan ya samu sabon mukamin a mawuyacin lokaci a tarihin kasar, lokacin da akwai matsalolin tsaro da yawa, yanada yakinin Ibrahim Idris zai aiwatar da aikin shi fiye da yadda ake tsamanni.

Muna sane da soyayyar ka ga adalci da gaskiya. Muna kuma sane da cewan abokan aikinta sun amince da kai sosai, saboda hka, muna addu’an wadannan kyawawan halayen naka su zama abin bege wajen gudanar da ayyukan ka a Ofis.” Ya ce.

Sarki Sanusi ya taya sabon Sifeto murna,ya bashi shawara
ibrahim idris

ibrahim idris, wanda tsohon Kwamishanan yan sanda ne na Jihar Kano,Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya nada shi sabon mukaddashin Sifeto Janar na yan sanda a ranar talata, 21 ga watan yuni.

Bayan nada shi, ya ba da umurnin cewa duk jami’in dan sandan da ya kai matsayin ‘Assistant Supritendent ASP zuwa Sifeto Janar, sai sun bayyan kadarorinsu.

KU KARANTA : Buhari ya yi kuskure a nadin shugaban ‘yan sanda –NOPRIN

Amma kungiyar kula ya gyaran yan sanda watau ‘Network on Police Reform in Nigeria (NOPRIN)’ ,tace Shugaban kasa, Muhammadu Buhari  yayi kuskure wajen zaben Ibrahim idris.

Asali: Legit.ng

Online view pixel