Alamomi 5 da ke nuna Messi zai koma ruwa

Alamomi 5 da ke nuna Messi zai koma ruwa

-Ikirarin Messi na barin kwallon a bisa takaici ne, zai iya sauyawa

-Madonna ya roki Messi kan shawarar da ya yanke

-Ritayarsa  babban lamari ne ga gwamnatin Argentina

Masoya wasan kwallo da yawa sun yi amanna da cewa ritayar da Messi ya ce zai yi daga kwallo ba za ta yiwu ba. Da akwai alamomi da suke nuna cewa gwarzon dan Barcelona zai koma bugawa kasar sa kwallo kamar haka:

Alamomi 5 da ke nuna Messi zai koma ruwa

Yanke shawara a lokacin da mutum ke cikin wani hali matukar farin ciki ko baki ciki na iya sauyawa idan hankali ya kwanta, don haka Messi na iya sauya shawara. Kiraye-kirayen da aka yi ta yi wa dan wasan na ya sake shawara ka iya tasiri. Cikin wadanda suka yi kira ga Messi sun hada da Maradonna da kuma dimbin magoya bayan dan wasan.

Alamomi 5 da ke nuna Messi zai koma ruwa
Messi da Maradonna ya na rarrashinsa

A yanzu dangantaka da tsakanin Messi da hukumar kwallo ta Argentina AFA ta yi tsami gabannin wasansu da Chille. Idan har aka yi garanbawul a hukumar, wannan ana ganin zai taimaka wajen sa dan kwallon watakila ya canza shawara.

KU KARANTA: Mikel Zai bar kungiyar kwallon kafa ta Chelsea

Mai tsaron raga Sergio Romero ne na farko da ya rarrashi Messi kan shawarar da ya yanke, ya na cewa ba’a biye wa aikin zuciya. Irin wannan rarrashi na abokan wasa na da tasiri, kuma za su iya Messi ya canza shawara.

Sa bakin na tasiri a kan ‘yan wasan da suka yi ritaya su dawo, kamar yadda shugaban faransa Nicolas Sarkorzy ya roki Zinedine Zidane da ya yi ritaya, da dawo ya bugawa kasar a gasar cin kofin duniya ta shakarar 2006 a Jamus. Hakan na iya faruwa ga Messi.

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel