Tsagerun Nija Delta sun bude wuta a Ogun

Tsagerun Nija Delta sun bude wuta a Ogun

– Wasu ‘yan bindiga da ake zargin tsagerun Neja-Delta ne sun buda wuta ga tawagar Gwamnan Jihar Ogun

 – Tsagerun sun hana Mataimakiyar Gwamnan Jihar, Princess Yetunde Onanuga ziyartar Garin Ebute – Ibafo da ke Karamar hukumar Obafemi Owode na Jihar

Tsagerun Nija Delta sun bude wuta a Ogun
Tsagerun Nija Delta

Jaridar ‘The Nation’ ta buga labarin cewa, wasu ‘yan bindiga da ake kyautata tsammani tsagerun Neja-Delta ne, sun buda wuta a Garin Ebute – Ibafo na Karamar hukumar Obafemi Owode, inda suka hana tawagar Gwamnan Jihar wucewa.

Mataimakiyar Gwamnar Jihar Princess Yetunde Onanuga wadda ke tare da Jami’an ‘Yan Sandan Kasar, Sojoji da kuma Jami’an DSS. Mataimakiyar Gwamnar dai ta je yankin ne domin ta duba tabargazar da aka yi. Sai dai tsagerun sun tare hanyar suka hana tawagar Mataimakiyar Gwamna, Princess Onanuga wucewa, ‘Yan Bindigan Neja-Deltan suka shiga buda wata, wannan ya sa dole sojojin suka ja-da-baya.

Sakataren Gwamnatin Jihar na Ogun, Mista Taiwo Adeoluwa, wanda shi ma yana cikin tawagar, yace dole Gwmanatin Tarayya ta shigo cikin wannan harka. Ace mataimakiyar Gwamna ba ta isa ta shiga wani yanki ba a Jihar, dole Gwamnatin Tarayya tayi wani abu. Inji Sakataren gwamnnatin Jihar. Mista Taiwo Adeoluwa yace wannan abu ya fi karfin hukumar ‘yan Sanda, sai an samu wata rundunar hadin gwiwa, kamar yadda aka yi a yankin Neja-Delt

Bayan dai hare-haren da ake ta kara samu a yankin Kasar na Neja-Delta mai azikin man fetur, Gwamnatin Tarayyar za ta aika wasu kwararrun sojoji daga Arewa maso gabashin Kasar zuwa yankin. Za a tura sojojin da suke fada da ‘Yan ta’adda na Boko Haram zuwa yankin na Neja-Delta.

Sai dai tsagerun Neja-Delta sun yi ma Shugaba Muhammadu Buhari kashedin zuwa yankin na Neja-Deltan Kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel