Kasar Iceland tayi waje da Ingila

Kasar Iceland tayi waje da Ingila

– Kasar Iceland ta kora Kasar Ingila gida a Gasar EURO 2016.

 – Kasar Iceland ta doke Ingila bayan ta fara shan kashi.

 – Kasar Iceland za ta gamu da Kasar Faransa a zagaye na gaba.

 

Kasar Iceland tayi waje da Ingila

An kora Kasar Ingila gida daga gasar kwallon kafan zakarun Nahiyar Turai na bana. Ingila ta sha kashi ne wajen Kasar Iceland, wanda babu wanda yayi tunanin za su tabuka wani abin kirki a gasar. Minti 4 da sa wasa Dan wasa Rooney Wayne ya ci ma Ingila kwallo, sai dai kafin aje ko ina, Ragnar Sigurdsson na Iceland ya rama ma Kasar Iceland a minti na 6. A minti na 19 kuma Kasar Iceland ta kara zuba ma Kasar ta Ingila kwallo ta dan wasa Kolbeinn Sigthorsson, Golan na Ingila dai ya gagara tare kwallon lamba taran (9) na Iceland, Sigthorsson.

Kasar Ingila dai tayi kokarin canza labarin, sai dai Kasar Iceland din ta cije. Iceland din ta tare bayan ta da kyau har aka tashi a haka, Kasar Iceland dai tayi nasara bisa Ingila da ci 2-1. Wannan sakamako yaba kowa mamaki. Yanzu dai Kasar Iceland za ta hadu da Kasar Faransa a wasan zagaye na gaba, inda kasashe 8 za su fafata. Iceland za ta gamu da Faransa a Ranar Lahadi. Abin dai kamar tatsuniya, Iceland tana ta kutsawa gaba a Gasar kwallon na Nahiyar turai, EURO 2016.

Idan ba a manta ba dai, a Kasar Faransa ne ake buga Gasar wasan na EURO a wannnan karo.

Asali: Legit.ng

Online view pixel