Wata Yar Najeriya ta janyo tashin tashina a Indiya

Wata Yar Najeriya ta janyo tashin tashina a Indiya

Wata yar Najeriya tare da kawarta sun janyo tashin hankali a wata Kasuwar Bengakaru a kasar Indiya bayan sun yi tatil da kayan maye.

Wata Yar Najeriya ta janyo tashin tashina a Indiya
Matar a lokacin da ake kokarin kamata

Yansanda Indiya sun yi nasarar kamata ne bayan tirka tirka mai tsawo da aka sha fama da ita, inda daga nan aka wuce da ita Asibiti don duba lafiyar ta. Yansandan sun tabbatar da cewa Yar Najeriyan da kawarta sun yi wannan aika aikan ne bayan su bugu daga kwayoyin da ake ganin suna saba sha.

An yi nasarar danne matar a kasa ne da taimakon da taimakon wata Yarsanda bayan ta ciccije wasu Yansanda, wanda haka yasa su ka garkame ta. Yansandan garin Bengaluru sun shigar da koke akan matan biyu day a shafi wuce gonad a iri, da kuma tada hankulan Mutane. Daga bisani kuma an kwantar da ita a Asibiti mai suna NIMAHNS.

Asali: Legit.ng

Online view pixel