Buhari ya gayyaci Dangote, Otedola da Tinubu shan ruwa

Buhari ya gayyaci Dangote, Otedola da Tinubu shan ruwa

– Shugaba Muhammadu Buhari ya sha-ruwa tare da manyan ‘Yan Kasuwan Kasar.

 – Shugaban yace an gano Jihohi 13 da za su iya noma shinkafar da Kasar za ta ci nan da shekara daya da rabi.

 – Shugaban Kasar yace bai ga wani amfanin rage darajar Kudin Kasar ba, har yanzu.

Buhari ya gayyaci Dangote, Otedola da Tinubu shan ruwa

 

 

 

 

 

 

Buhari yayi buda-baki tare da hamshakan ‘Yan Kasuwar Najeriyar. Shugaba Muhammadu Buhari yayi buda-bakin Sa jiya ne tare da manyan ‘Yan kasuwan Kasar a fadar gwamnati da ke Birnin Tarayyar Abuja. Shugaba Buharin yayi buda bakin azumin Ramadan ne dai tare da gawurtattun ‘Yan Kasuwar Kasar, wanda suka hada da: Femi Otedola Alakija, Tony Elumelu, Alhaji Aliko Dangote, Jim Ovia, da kuma Wale Tinubu.

Da shugaban Najeriyar yake magana, yace gwamnatin sa ta kama hanyar ganin cewa Najeriya ta noma shimkafar da zata ishe ta nan da watanni 18. Buharin yace, Minastan Harkar noma na Kasar, Audu Ogbeh ya gano Jihohi 13 na Kasar da za su iya noma shinkafa. Shugaban Kasar yace an dade a da ana barnar arzikin Kasar ana shigo da kayan abinci. Buharin yace idan dai ba ayi gyara ba yanzu, to za ayi ta fama da wahala gaba. Game da karya darajar Naira kuma, Shugaban Kasa Buhari yace har yanzu bai gamsu da amfanin hakan ba. Ya tambayi ko me hakan zai tsinana ma Kasar. Sai dai yace shi ba masanin tattali bane, kuma ba dan kasuwa bane, saboda haka bai gamsu da duk bayanan da aka masa ba.

Hagu-Dama: Shugaban man ‘Oando’, Wale Tinubu; Alhaji Aliko Dangote mai Dangote; Mr. Jim Ovia na Zenith Bank da kuma Mista Tony Elumelu lokacin da suka sha ruwa tare da Buhari.

An yi buda-bakin ne a dakin ‘Banquet Hall’ dake Babban Birnin Tarayya, Abuja. Kola Jamodu, shugaban kamfanin Unilever yayi magana a madadin sauran ‘yan kasuwar, ya mika godiyar su ga Shugaba Buharin da ya gayyace su shan ruwa. Kuma ya tabbatar masa da cewa ‘yan kasuwan Kasar a shirye suke da su taimaka wajen gyara tattalin arzikin Kasar.

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel