Buhari na fushi da sabuwar manufar CBN

Buhari na fushi da sabuwar manufar CBN

-     Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa sabon manufar da babban bankin kasan ta kawo, bai amfani tattalin arzikin kasan ba.

-    Buhari ya siffanta hakan a matsayin rage darajar kudin Najeriyar ne.

 -   Buhari ya kalubalanci yan kasuwa da su samo ma mutane aikin yi.

Jaridar Vanguard ta bada rahoton cewa, Shugaba Muhammadu Buhari yace sabon manufar kudin da babban bankin Najeriya CBN ta gabatar, bai amfani tattalin arzikinmu ba. CBN ta kawo wannan manufan ne domin kasuwa ta sanar da mu darajar naira. wannan sabon manufar, an yi shine domin rage darajar Naira ta bayan gida. Amma buhari yace shi har yanzu bata amfani kasa ba.

Buhari na fushi da sabuwar manufar CBN

Shugaban Kasan yayi maganan ne bayan taron buda bakin na watan Ramadana tare da mambobin kungiyar al'umman manyan ‘yan kasuwa a fadar Shugaban Kasa a Abuja.  Shugaban kasan yace: “Bani jin dadin sakamakon da nike samu daga babban bankin najeriya a bisa rage darajar naira. Amfanin meye rage darajar ta mana a shekarun baya? A watan Agusta 1985, Naira na N1.3/$ amma yanzu N300 ko 350/$. menene amfanin hakan? Amfanin meye zamu samu daga rage darajar naira. Ni ba masanin tattalin arziki ba ne, haka zalika ni ba dan kasuwa bane, ni ban fahimci abun da yan tattalin arzikin ke nufi ba. Wannan abin yanzu shi ne sanadiyar rugujewan tattalin arzikin kasa.

Amma,  Buhari ya kalubalanci yan kasuwan da su samawa mutane aiki a kasuwa

KU KARANTA : Kungiyar CAN sun kai hari ga Shugaba Buhari

Yace daga cikin dabarun sarrafa tattalin arzikin, an gano Jihohi 13 da zasu iya sarrafa shinkafan da zata ciyar da kasa gaba daya na tsawon watanni 18.  Ya yarda da maganan cewa yan kasuwan za su shiga kunci , sanadiyar kasancewan abubuwa kaman Shinkafa, Tumatur, Alkama da ake shigowa da su, za'a fara yin su a gida Najeriya.

Kafin yanzu,  Buhari ya fada a watan fabrairu, a kasan masar cewa baya goyon rage darajar naira, yace najeriyar da bata fitar da komai zata shiga halin kakanikaye idan ake rage darajar naira. Hakazalika a watan maris, a kasar kenya, ya jaddada cewan ba zai kashe naira ba.

Amma a ranar 2 ga watan yuni, Shugaba Muhammadu Buhari ya bada goyon bayan dabarar da CBN ta kawo na sakin naira a kasuwa.

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel