Yan bindiga sunyi garkuwa da wani babban akawu a Ondo.

 Yan bindiga sunyi garkuwa da wani babban akawu a Ondo.

-   Wasu Yan bindiga sun yi garkuwa da babban akawun cibiyar kiwon lafiya tarayya watau ‘Federal Medical Centre (FMC)’ Mr. Kayode Asaju, a garin Owo, Jihar Ondo.

-    Mumunan abun ya auku ne da yammar lahadi, 26 ga watan Yuni.

-    Anyi garkuwa da asaju ne yayinda ya ke balaguro a karshen makon da ya gabata.

Jaridar Tribune ta samu masaniyar cewa yana bulaguro zuwa Abuja domin halartan wani taro da za'ayi a ranar litinin 27 ga watan yuni, sai akayi garkuwa dashi a babban titin Lokoja zuwa Abuja a ranar lahadi, 26 ga watan yuni.

An bada rahoton cewa Yan bindigan su akalla guda 5 ne, sunyi garkuwa dashi ne cikin daji.

 Yan bindiga sunyi garkuwa da wani babban akawu a Ondo.

Game da wata majiya, yan bindigan sun isar da sako zuwa ga iyalen shi ,musamman matar shi cewa suna rike dashi. Matar, wacce ke aiki a wajen aiki daya da shi a Federal Medical Centre (FMC). Sun bukaci a basu naira N5 miliyan kudin fansan sa.

KU KARANTA : Yadda yan bindiga suka kasha mijina- Mrs Buhari

Kakakin jami'an yan sandan Jihar Ondo, Mr. Femi Joseph, yayinda yake magana akan abinda ya faru, ya bayyana cewa abun takaicin ya faru a wajen Jihar sa ta Ondo ne, Amma ya na bada tabbacin cewa jami'an yan sandan Jihar Ondo zata hada kai da ofishin yan sandan Jihar Kogi domin tabbatar da cewa an ceco Mr. Kayode Asaju , an kai shi wajen iyalan shi cikin koshin lafiya.

Kusan mako 1 daya gabata, kiris ya rage a yi garkuwa da sarkin gargajiyan masarautar Gbaramatu da ke yankin Neja Delta, a hanyar komawa fadar sa tare da matarsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel