Mutane 5 da zasu iya gadar Messi

Mutane 5 da zasu iya gadar Messi

Messi dai shahararren dan wasa ne da ake tunanin ba'a taba yin irin sa ba a kasar Argentina. Messi ya aje buga wa kasar sa wasa ne wanda kuma hakan ya jefa kowa cikin mamaki.

Mutane 5 da zasu iya gadar Messi
Messi

Amma kasar ta Argentina ta shahara wajen yaye shahararrun yan wasa kafin Messi din ko ma maradona wanda ake tunanin ba za'a tsaya akan sa ba. Tambayar da take ta yawo a bakunan jama'a dai yanzu itace shin waye zai iya maye gurbin na Messi?

Ga wasu 5 nan da aka lissafa:

1. Angel Correa: Duk da cewa shekarar sa 21 kacal, dan wasan tsakiyar na kulob din Atletico Madrid zai girgije ya kuma zama shahararre nan gaba.

Sau dayawa dai akan kamanta dan wasan da Carlos tevez saboda yadda yake da karfi da gudu sosai.

2. Paulo Dybala: Duk da dan wasan na kulob din Juventus bai samu shiga wasanni sosai ba a wannan gasar da ta gabata, amma ya taimaka ma kasar tasa duk lokacin da ya shiga fili a matsayin dan canji.

Duk kuwa da kasancewar dan wasan na tsakiya amma hazakar sa ta cin kwallaye zata taimaka masa sosai.

3. Erik Lamela: A lokuta da dama dan kulob din na Tottenham Hotspurs yana taimaka ma kasa har da ma kulob din nasa. Wannan ne ma ya janyo masa yabo sosai da masoya da dama .

Duk da dai kuma ya fara suna ne bayan shekarun sa sun dan ja, ana kyautata zaton zai yi tasiri sosai a kasar tasa saboda iya kwallon sa.

4. Javier Pastore: Dalili daya da har yanzu yake zama a benci shine saboda wuri daya suke bugawa da Messi din. Dan wasan PSG din yana da duk wata kwarewa da ake bukata wajen dan wasan tsakiya kuma ana kamanta shi ma da Zidane.

Pastore ya kan buga wurare da dama da suka hada da gaba tsakiya da ma gefen fili.

5. Angel Di Maria: Tasu tafi zuwa daya ma dai da Messi a duk yan wasan na Argentina don kuwa sun zura kwallaye dayawa tare da taimakon juna.

Bayan kuma daman shine zai anshi shugabancin yan wasan kasar, kasarcewar shi cikin fili ma kawai wani abun kwarin gwiwa ne ga sauran yan wasaan.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel