A Binciki Burutai yanzu - Falana, Afenifare

A Binciki Burutai yanzu - Falana, Afenifare

-Kungiyoyi da shahararun yan’Najeriya sun yi kira ga cikakken bincike na shugaban ma’aikatan sojoji, Lt. Gen. Tukur Burutai da hukumar yaki da cin hanci da rashawa wato EFCC ke yi

-Falana yace ba hurumin sojoji bane yin Magana da yawun Brutai a kan zargin

A Binciki Burutai yanzu - Falana, Afenifare

Kungiyoyi da kuma shahararun yan’Najeriya sun yi kira ga cikakken  bincike na shugaban ma’aikatan sojoji, Lt. Gen. Tukur Burutai da hukumar yaki da cin hanci da rashawa  wato EFCC ke yi kan siyan kadarori na dala miliyan $1.5 a kasar Dubai, United Arab Emirates.

Sahara Reporters sun rahoto cewa shugaban sojojin da matan sa guda biyu sun mallaki kaddarori na dala miliyan $1.5 a kasar Dubai.

KU KARANTA KUMA: Kungiyar Niger Delta Commandos (NDSC) sun gargadi Buhari

 Daraktan SERAP, Adetokunbo Mumuni  yace idan ana so a ga adalcin hukumar yaki da cin hanci da rashawa. Dole ne hukumar ta duba da idon basira , shin Burutai na da kudin da zai iya mallakan kaddarorin a matsayin san a ma’aikacin farar hula.

Yace: “maganan na hannun hukumar EFCC da kuma hukumar ICPC don yin binciken COAS. Shin Burutai da matansa guda biyu sun biya kudin kaddarorin a lokaci guda ne a kasar Dubai? A matsayin san a ma’aikacin farar hula, nawa yake karban albashi a wata? Albashinsa ya isa ya mallaka mai wannan kaddarorin? Idan har hukumar yaki da cin hanci da rashawa na so a dauke ta mai adalci ba wai mai zaben wanda zata hukunta ba, ya zama dole tayi bincike akan Burutai. Hakkin ta ne aikata hakan.”

Haka zalika, sakataran kungiyar Afenifere na kasa, Yinka Odumakin, ya bayyana wa jaridar Punch cewa Buhari ya binciki Burutai a kan zargin kaddarorinsa na kasar Dubai.

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel