An kori yan Gana Miliyan daya daga Najeriya

An kori yan Gana Miliyan daya daga Najeriya

A wannan rahoto na tuna baya, Legit.ng ta yi dubi ne akan yadda korar kare da aka yi wa Jama’ar Kasar Gana mazauna Najeriya a shekara 1983 wanda yawan su ya kai mutum Miliyan daya, Najeriya tayi zargin cewa yawancin Jama’an bakin haure ne. Wannan hukunci da kasar Najeriya ta dauka ya girgiza duniya, saboda ana tunanin ai Najeriya da Gana makwabta ne na kud-da-kud, kuma dangantakar kasashen ya samo asali ne tun gabanin zuwan Turawan mulkin mallaka Afirka.

An kori yan Gana Miliyan daya daga Najeriya

A lokacin kuwa Najeriya tana tsakar cin moriyar kudin da take samu daga tashin gwauron zabi da farashin kudin mai yayi. Koda yake ana mitar cewa su Yan Gana mazauna Najeriya sun mamaye duk wani aikin Yan Najeriya za suyi, ana cikin haka ne kwatsam sai farashin mai ya fadi warwas, hakan ya sa kasar Najeriya ta shiga matsanancin hali, dalilim da yasa kenan kasar ta huce haushin ta akan yan Gana.

Yan Najeriya sun yi murna matuka lokacin da aka sanar da wannan da korar, su ko yan Gana, bacin rai ne kawai da ba zasu taba mantawa ba. An yake musu har zuwa 10 ga watan Mayu da zasu fita, ko kuma duk day a sa me su, su suka ja ma kan su. Cikin sanarwan da Gwamnatin Najeriya ta fitar, tace “Idan basu bar Najeriya ba, a kama su, kuma a kais u kotu, sa’annan a mayar dasu kasar su a tilas, bari ma, bai ma kamata mu basu wani uzuri ba”

Anyi zargin cewa matakin da Najeriya ta dauka baya rasa nasaba da matsayin da kasar Gana ta taba dauka kwatankwacin wannan a shekarun 1970 zamanin Shugaba Kofi Abrefa Busia, inda aka umarci duk wanda ba yan asalin kasar ba da su fice daga su barta, yawancin Jama’an da aka kora yan Najeriya ne. a nan Najeriya an rika cika manyan Motoci da Jirgin ruwa mai daukan kaya da yan Gana, sa’annan aka sanya Sojoji das u sa ido, su tabbatar kowannen su ya ba Najeriya. Yawancin Mutanen sun tafi sun bar Kadarori da Arzikin su saboda rashin samun takardun zama daga Gwamnatin Najeriya.

Gwamnatin kasar Ganata wannan lokacin tayi tofin Allah tsine da nuna bacin rai “Najeriya ta ji kunya, wannan mataki da Najeriya ta dauka ya saba da tsarin kungiyar hadin kan kasashen Afirka”,nan da nan Kalmar ‘Ghana must go’ ya zama abin raha tsakanin yan Najeriya, suna ganin Gwamnatin Shagari tayi abin day a kamata. Sun sa ran cewa korar mutanen Gana daga Najeriya zai kawo samun aikin yan Najeriya, sai dia Kash! Wannan zato na yan Najeriya bai tabbata ba.

Tafiyar yan Gana bai sa Najeiya ta zama wata madaukakiyar kasa ba kamar yadda ake zato, sai dai ma yan Najeriya sun gano wasu gaga gaggan matsaloli ne wadanda ma sun fi karfin batun mamaye ayyuka da ake cewa yan Gana sun yi. Ya zamto yan Najeriya bas a iye yin Ire-iren kananun ayyukan day an Gana ke yi a baya, saboda basu saba da ayyukan ba, sa’annan kuma wasu daga cikin Yan Ganan suna tafiyar da kananan masana’antu ne, inda tafiyarsu ta jawo kullewar ire iren masana’antun, kuma Gwamnatin Najeriya bata yi wani yunkurin farfado da su ba.

Har karshen 1983, kasar Najeriya bata samu wani canjin azo a gani ba, yan Najeriya na nan jiya I yau, daga nan ne aka fara tunanin cewa akwai babbabr matsalar dake damun tattalin Arzikin kasar. A ranar 31 ga watan Disamba 1983 Janar Muhammadu Buhari ya kwace mulki, inda ya jingina hujjarsa ta yin haka ga irin Almundaha, da cin hanci da rashawar dake gudana a karkashin Gwamnatin Shagari.

Toh Jama’a kuna ganin cin hanci da rashawa shi ne matsalar Najeriya a 1983? Sai mun ji ra’ayoyinku a sashen ra’ayi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel