Bazamu sallama wa Fulani makiyaya jihar Benue ba-Ortom

Bazamu sallama wa Fulani makiyaya jihar Benue ba-Ortom

-Gwamnan Ortom yace jihar Bunue bazata bazata yarda da wajen kiwon dabbobi a fili ba

-Ortom ya bayyana cewa gwamnati zata ci gaba da ba da tallafi ga wadanda suka shirya kiwon shanun su a jihar

-Gwamnan yace  har ilah yau aikin noma shine babban masana’anta a jihar Benue

Bazamu sallama wa Fulani makiyaya jihar Benue ba-Ortom
Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom

Gwamnan jihar Benue Samuel Ortom ya bayyana cewa wani dokana hana kiwon dabbobi a fili zai fara aiki a jihar sa nan ba da jimawa ba. Gwamnan yayi wannan sanarwan ne a Makurdi, babban birnin jihar Benue, a ranar Litinin 27 ga watan Yuni, a karshen taron da akayi  tare da masu ruwa da tsaki a yankunan jihar guda uku.

A cewar sa, gwamnatin sa bazata sallama jihar Benue ga Fulani makiyaya da suka mamaye ko in aba, duk da dubin hare-hare da suke kai wa jihar, jaridar Vanguard ta ruwaito. Duk da haka, Ortom ya bayyana cewa gwamnatin sa zata ci gaba da tallafa wa wadanda suka shirya killace kiwon dabbobinsu a jihar.

Gwamnan ya ce har ila yau aikin noma yana ci gaba da zama babban masana’anta a jihar, cewa abin lura shine, kasar jihar bazata iya daukan nauyin aikin noma da kuma kiwon dabbobi a lokaci guda ba.

KU KARANTA KUMA: Dan achaba ya kashe kansa saboda rashin haihuwa

Gwamnan yayi jimami tare da iyalan wadanda suka rasa yan’uwansu a lokacin harin da Fulani makiyaya sukayi, ya kuma tabbatar masu da cewa gwamnatin sa tana kokari dan ganin cewa zaman lafiya ta warzu a fadin jihar.

Karamar hukumomi takwas a jihar Benue, wanda ya hada da, Agatu, Buruku, Guma, Gwer-west, Logo, Kwande, Gwer-East da kuma Katsina-Ala, ne suka samu hari daga Fulani makiyaya.

An rahoto cewa kimanin mutane 300 zuwa 500 ne aka kashe a karamar hukumar Agatu da sauran hukumomi a jihar Benue, cikin watan Maris.

 

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel