An gwada Jirgin kasa daga Abuja zuwa Kaduna 

An gwada Jirgin kasa daga Abuja zuwa Kaduna 

-Baibai da tsohon jirkin kasa, maraba da sabon jirgin kasa a Najeriya                                                                

-Dadadden hanyar jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna da aka dade anayi an gama shi, wanda zai fara aiki wannan watan.                                                                                       

Daya daga cikin wadanda suka fara gwada wannan hanyar jirgin shine wani aminin Shugaba Buhari wato Bashir Ahmad, mataimakin shugaba Buhari akan sabon kafar yada labarai, Ennesi Hassan. Malam Hassan ya tura hotunan sa ayayin da yake tafiyar sa na farko a cikin jirgin.

An gwada Jirgin kasa daga Abuja zuwa Kaduna 

Hanyar ta jirgin daga Abuja zuwa kaduna tanada tsawon kilomita 186 wanda ta mike a shimfide kuma a tsaye daga idu, kusa da garin Abuja zuwa kaduna a Arewacin Najeriya. Yanada wurin yada zango har guda 9 sannan yanada wurin zaman mutane kuma yanada wajen ajiyan kayayyaki duk a ciki. Kamfanin China Railway Construction Corporation suka yi shi akan kudi dalar amurka miliyan 850 acikin shekaru uku.

Hanyar jirgin Abujan zuwa Kaduna shine na farko chikin hanyoyin jiragen kasa na nageriya  na zamani da muke dasu a kasar nan. Jirgin kasan da zaiyi zirga zirga an kaiyade masa gudun da zaiyi wanda bazai wuce gudun kilomita 200 zuwa 250 a awa daya. Tafiyar daga Abuja zuwa Kaduna inda aka rage awa daya sannan jiragen suna iya daukar fasijoji har guda 5000.

Hanyar jirgin ta hada da babban birnin tarayya zuwa inda zata dunga yin kasuwanci  zuwa Kaduna, zai zamanto tafiya mafi sauri dasuka hada da safaran kayayyaki da kuma mutane wanda zasu hada biranen guda biyu.

KU KARANTA : Amaechi da Kachikwu sun samu sabani a cikin jama’a

Bayan samar da wannan sanannen hanyar jirgin na zamani ga al'umma, hanyoyin jiragen Najeriya koma baya saboda rashin gyara dakuma kulawa.Amman duk da haka bude wannan sabon titin jirgin mai sauri shima wani cigaba ne na taka wani mataki a hukamar ta kula da jiragen kasa, sannan akwai burin bude wasu hanyoyi jirage kasa wanda zasu hada da makotan wannab kasar nan gaba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel