Yadda za'a kafa Biafra ba tare da yaki ba

Yadda za'a kafa Biafra ba tare da yaki ba

Jawabin Edita: Bayan ficewar Birtaniya daga Kungiyar ‘EU’ ta nahiyar Turai, abin da aka fi sani da BREXIT, Masu neman Kasar Biafra (Kungiyar IPOB) sun sanar da cewa suma za su fara kokarin neman nasu BIAFREXIT. Kess Ewubare, babban Edita a Naij,com, ya bayyana yadda mutanen Kasar Ibon da duk masu neman Biafra za su ci hakar su ba tare da an kashe ko kuda ba.

Yadda za'a kafa Biafra ba tare da yaki ba
Ojukwu, 

Fadin Duniya ta yi mamaki lokacin da Kasar Birtaniya ta zabi ta bar Kungiyar Nahiyar Turai watau ‘European Union’ a ranar Alhamis 23 ga watan Yunin nan. Kaso kimanin 52% na ‘yan Kasar su ka zabi su fice daga cikin Kungiyar ‘European Union.’ Bayan hakan ne Firayim Minista Cameron, ya sanar da cewa zai sauka daga ragamar mulki. Wannan mataki dai da Birtaniya ta dauka yana cikin manyan matakin da Kasar ta dauka tun bayan Yakin duniya na biyu. Ficewar Birtaniya daga ‘European Union, EU’ yana da tasiri ga tsarin karbar ‘yan ci-rani, da ma tattalin arzikin Kasar.

‘Yan Najeriya ba za su rasa daukan darasi ba daga matakin na BREXIT, wanda wasu bangaren mutanen Kasar ke neman ballewa daga Najeriyar. Sai dai ita ‘Kungiyar EU, European Union’ gamin tattali da siyasa ne da suka kunshi Kasashen Turai guda 28, BIAFREXIT kuma yunkurin neman Kasa mai ‘yanci ne daga cikin Kasar Najeriya suna ganin an maida su saniyar ware a Kasar. Kokarin neman Kasar Biafra yana da asali tun daga Shekarar 1966, lokacin da wasu Inyamurai daga cikin sojin kasar (wanda wani Manjo Nzeogwu ya jagoranta) suka hambarar da gwamnatin Kasar, suka karkashe Shugabannin (Kudu-maso-yamma da Arewacin) Kasar. Sai dai juyin mulkin bai yiwu ba, inda Manjo-Janar JTU Aguiyi-Ironsi, shi ma inyamuri ya karbi mulkin

Sai dai bayan Manjo-Janar Ironsi ya hau mulki, sai bai hukunta wadanda suka kashe Shugabannin Kasar ba. Wannan ya sa ‘yan Arewar suka harzuka, suka shiga tada rikici, a yankin a cikin watan Mayun 1966. Wannan yayi sanadiyyar kashe Inyamurai da dama dake Arewacin Kasar. Jim kadan Sojojin Arewacin Kasar suka kifar da Gwamnati a ranar 29 ga watan Yulin Shekarar 1966. A wannan juyi ne aka kashe Manjo-Janar JTU Ironsi da ma wasu manyan Sojojin Kasar. Daga nan kuma Laftan-Kwanal Yakubu Gowon, wani dan Arewa ya karbi mulki. Sai dai wannan bai kawo karshen kisan Inyamuran ba a yankin Arewa har karshen Satumban 1966.

 

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel