EFCC ta kwace kadarori 29 daga hannun sojin sama

EFCC ta kwace kadarori 29 daga hannun sojin sama

A cigaba da kokarin da take yi wajen haki da cin hanci da rashawa, hukumar EFCC ta kwace kadarori akalla 29 daga hannun wani tsohon sojin saman Najeriya.

EFCC ta kwace kadarori 29 daga hannun sojin sama
efcc

Kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito, cikin tsaffin sojojin da abun ya shafa hadda tsohon shugaban sojin saman Najeriya Adesola Amosu, tsohon akawun sojin saman da kuma tsohon shugaban bajet din Air Vice Marshal Jacob Adigun da kuma Commodore Olugbenga Gbadebo.

Kadarorin 11 ne dai aka kwace daga hannun Amosu, 12 kuma daga Adigun sannan 6 daga hannun Gbadebo. Wasu kadarorin da aka kwace daga hannun Amosu sun hada da gida dake titin Adeyemo Alakija, Victoria Island, Lagos mai darajar N250m, da ma wani mai darajar N110m shima a Lagos din sai kuma wani mai darajar N33m a garin fatakwol dadai sauransu.

Kadarorin kuwa da aka kwace daga hannun Gbadebo sun hada da wata gonar kifi mai darajar N10m da wata gonar kaji mai darajar N20m dake Lagos da ma wata makaranta. Tsofaffin sojojin dai ana zargin su ne da laifin karkatar da kudaden alumma da suka kai darajar N21b a shekarar 2014. Tuni dai har hukumar ta EFCC ta makasu kotu a garin Abuja.

Cikin zargin da ake musu hadda karkatar da kudaden alumma wajen aikata haram da kuma safarar kudaden da suka wuce kima. Lauyan masu gabatar da karar Rotimi Oyedepo Isiokuwa ya ce mutane 42 ne zasu bada shaida a kotun.

Asali: Legit.ng

Online view pixel