Labari da dumin sa: Saraki da Ekweranmadu sun Gurfana a gaban Kuliya

Labari da dumin sa: Saraki da Ekweranmadu sun Gurfana a gaban Kuliya

Shugaban majalisar Dattijai Sanata Bukola Saraki da mataimakinsa Ike Ekweranmadu sun gurfana a gaban Kuliya manta sabo in da ake tuhumar su da tsara jabun dokoki na Zaben Shuwagabannin Majalisa.

Labari da dumin sa: Saraki da Ekweranmadu sun Gurfana a gaban Kuliya
Saraki da Ekweranmadu a lokacin da suka shigo kotu
Labari da dumin sa: Saraki da Ekweranmadu sun Gurfana a gaban Kuliya
Tirka tirka tsakanin Yan Jaridu da yan sanda

Ku biyo mu don jin yadda ta kasan ce gaba gaba a kotun a safiyar yau.

9:16: Alkali ya bukaci Saraki da Ekweranmadu das u koma wurin zamansu na mintoci

15, saboda hayaniya da yayi yawa da cikowar da aka yi a cikin dakin sharia’ar

9:25: Har yanzu dai hayaniya ya ci gab a cikin kotun, a in da akawu akawun kotun keta kokarin kawo karshen hayaniya a dakin. Wani Akawu yayi kiran sunayen lauyoyin da Karar ta sha fa. An samu rohoton cewa wani Dan-sanda dake gadin Saraki ya daki wani Dan-Jarida saboda yunkurin da yayi na dauko hoton Shari’ar

9:29: Saraki ya shigo kotu kuma ya zauna, ya sha Farar Babbar Riga da Hula. Ekweranmadu ma ya zauna a gefen Saraki sanye da tufafin gargajiya irin na Inyamurai da Jar Hula. Hakanan  ma Stella Oduah, Dino Melaye da sauran Yan majalisa sun samu halarta.

9:38: Alkalin ya shigo, Jama’a da yawa na tsaitsaye ciki har da Yan Jaridu da lauyoyi da dama, kodai masu goyon bayan wandanda ake kara ko kuma akasin haka.

9:40: Dukkanin wadanda ake kara sun gurfana gaban Kotu cikin inda Shedu ke tsayawa.

9:53: An samu rudani cikin kotun inda lauyoyi daban daban biyu suka fito domin kare wand ake kara na Farko, tsohon Babban Akawun Majalisa.  Lauya Magaji Mahmoud ya tsaya don kare wanda ake kara na 1 da na 2, kwatsam sai ga wani Babban lauya Ikechukwu Ezechukwu ya furta cewa shima yana kare tsohon Akawun ne. daga karshe dai lauyoyin biyu sun sasanta tsakanin su.

Lauya Mahmood ya roki kotu da ta batar da bayyanr sa, ya ce “ina rokon Kotu ta bani dama mu sasanta wannan, ina fatan bayyana na a nan zai isar ma wanda ake kara na farko” in ji mahmood. Mahmoud ya bukaci kotun da ta watsi da gabatarwar da aka shigar a madadin wanda ake kara na farko. Saraki da Ekweranmadu da sauran mutane guda biyu sun gabatar da kariyarsu akan laifuffuka guda biyu da ake tuhumarsu dashi na tsarawa da yin amfani da Jaun dokoki wurin zaben Shuwagabannin Majalisa, Dukkanin wadanda ake kara sun musanta aikata laifin.

Bayan kotun ta saurari Lauya mai kara sai Lauyan wanda ake tuhuma ya sanar da kotu game yunkurin neman belin wadanda duke kare da suka mika. Nan fa Lauyan masu kara Muhammadu Diri yayi wuf ya ce ai shima yana da kishiyar wannan bukata da suka gabatar. Diri ya bukaci kotu da ta bada saurara da sauraren kararrakin na tsawon awa guda. Ganin Lauyan wadanda ake kara bai musanta wannan bukata ba, sai Alkali Yusuf Halilu ya dakatar da zaman na tsawon awa daya.

10:53: Bayan awa daya, Alkali ya shigo kotu. Sai Lauyan masu kara Diri yayi godiya ga kotu. Diri ya kara da cewa sun cimma dalilin daya sa suka nemi a tsahirta. Shiko Lauyan wadanda ake kara, Ezechukwu yace manufar belin da suke nema, shine domin wadanda ake kara su shirya ma Shari’ar.

Ezechukwu ya kara da cewa, Zancen da Lauya mai kara yayi na cewa wai shi wanda ake kara na farko zai iya gudun ma shari’ah zancen ne mara tushe. Ya ce “Ya maigirma mai Shari’a, mun riga mun san cewa ba’a taba kama ko damke wanda ake kara na farko ba, kuma ya kasance bai taba fashi ba a kullum, a gaba daya lokacin da ake yin bincike.”

Shima Lauya mai Kare Saraki y ace bukatar lauya mai kara cewa kada kotu ta bada belin Shugaban majalisar dattijai ba zancen da kotu za ta dauka bane, domin ai Sarakin yana fuskantar Shari’ah a katun da’ar ma’aikata-CCT, kuma bai taba fashi daidai da rana daya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel