Atiku da Ameachi ne manyan masu laifi –Lamido

Atiku da Ameachi ne manyan masu laifi –Lamido

-Tsohon gwamna jihar Jigawa Sule Lamido ya ce rigingimun PDP alamar karfi ne

-Yan APC ne ke da manya-manyan masu laifi saboda daga PDP suke, a cerwasa.

-APC da taimakon PDP ta ci zabe?

A martaninsa ga furucin shugaban jamiyyar APC, tsohon gwamnan jihar Jigawa Sule Lamido ya ce, manya-manyan ‘yan jam’iyya mai mulki APC, su ma manyan masu laifin ne, tun da tsaffin ‘yan PDP ne.

Tsohon gwammnan na mayar da martani ne ga furucin Cif John Oyegun shugaban jam’iyyar APC wanda ya ce muggan laifukan da ‘yan jam’iyyar PDP suka aikata a lokacin da jam’iyyar ke mulki, su suka jefa kasar nan a halin da ta ke ciki na lalacewar tattalin arziki.

Atiku da Ameachi ne manyan masu laifi –Lamido
Wani tsohon gwamnan jihar Jigawa daga 2007 zuwa 2015 mai suna Sule Lamido

Jaridar Daily Post wacce ta ba da labarin martanin tsohon gwamman ta ce, Sule Lamido ya fadi haka ne a yayin hirarsu da ‘yan jarida a Bamaina da ke karamar hukumar Birnin Kudu, a jihar Jigawa. Ta kuma rawaito shi ya na cewa; “I dan PDP ta aikata manyan laifuka a shekarunta 16 na mulki, to lallai mutane irin su Rabiu Musa kwankwaso, da Aliyu Wamakko, da Rotimi Ameachi, da Aminu Tambuwal, da Ganduje, da kuma Atiku, duk manyan masu laifi ne saboda tsaffin ‘yan PDP ne.”

KU KARANTA: Jam’iyyar PDP ta dakatar da wani dan takaran Gwamna.

Gwammnan ta bayyana irin rigimar da jam’iyyar ke fama da ita alama ce ta karfi, domin a cewarsa, PDP ita ce jam’iyya daya tilo da ta kunshi kowa da kowa daga lungu da sako na Najeriya. Sannan ya jaddada cewa PDP ce za ta kafa gwammnati 2019, kuma zai fito takara.

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel