Jihohi 4 basu da macancancta jakadanci- SGF

Jihohi 4 basu da macancancta jakadanci- SGF

- Sakataren gwamnatin tarayya , Babachir David Lawal , ya ce akwai Jihohi 4 da basu cancanci jakadanci ba.

-   Yace Mas'alan da majalisan dattawa ta kawo bai taka kara ya karya ba.

-   Sakataren ya bayyana cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya bi ka'ida wajen tara jerin sunayen.

-   an aika jerin sunayen majalisan dattawa ne ranan alhamis 9 ga watan yuni.

Sakataren gwamnatin tarayya, Babachir David Lawal, ya bayyana cewa jihohin Flato, Ebonyi, Ondo da Bayalsa basu da macancanta kujeran jakadancin kasa. Jihohin guda 4 basu da yan diflomasiyyan da zasu gudanar da aiki huldan kasa da kasa da suka cancanci kujeran. Jaridar Cable ta bada rahoto.

Jihohi 4 basu da macancancta jakadanci- SGF

Yayinda ya ke magana a wata hira tare da manema labarai a karshen mako, lawal ya bayyana cewa akwai ka'idojin da Gwamnati ta shirya na zaben jakadun, kuma Shugaba Muhammadu Buhari ya bi wadannan ka'idojin sau da kafa, sabanin abinda majalisa dattawa ke rayawa. Lawal ya ce mas' alar da suka kawo abu ne wanda bai taka kara ya karya ba, abune da za iya magana ta wayan sadarwa.

“Daga cikin jihohi 36 da babban birinin tarayya,kudin tsarin mulki tayi ta bada shawaran ayi daidai wa daida wurin raba mukamai, amma ba ta ce wajibi ne sai kowani jiha ta samu a kowani lokaci ba, kujeran ministoci ne kawai togaciya anan. Saboda haka, an bi shawaran kundin tsarin mulkin da gaske tunda an zabi jakadai 32 cikin jihihohi 36 da Abuja. Ina da yakinin duk mai idon basira zai yarda da wannan.Yace.

Sakataren ya kara da cewa zai amsa gayyata da majalisan dattawan ta masa a ranar 11 ga watan Yuni, kwamitin ta gayyace shi tare da Ministan harkokin waje, Geoffrey Onyeama,domin amsa tambayoyin yan majalisan .  Lawal ya nuna rashin jin dadin sa shi kansa saboda rashin wasi jihohi 4 sakamakon wasu dalilai da suka shafi diflomasiyya, amma ba son rai bane ko nuna fifiko.

KU KARANTA: Wani Sanata ya kushe sunayen Ambasadojin Buhari

Majalisa ta tuhumci jerin sunayen

A makon da ya gabata, Majalisan Dattawa ta dakatar da tantance Jakadu 47 da Shugaba Muhammadu Buhari ya kaddamar domin tabbatarwa a ranan 9 ga Yuni. Majalisa dattawa ta hangi rashin gaskiya da adalci wajen zabensu domin haka, ta yi kira  ga Sakataren gwamnati da ministan waje domin suyi bayanin abinda yasa hakan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel