Femi Adesina ya maganta akan Buhari

Femi Adesina ya maganta akan Buhari

Jawabin Edita: Femi Adesina shine mai ba Shugaban Kasa Muhammadu Buhari shawara kan harkokin watsa labarai. Ya tattauna game da batutuwan da suka shafi; siyasa, tattali, ta’addaci da sauran abubuwan da suka shafi Kasar ta Najeriya.

Femi Adesina ya maganta akan Buhari

 

 

 

 

 

 

 

 

Mai ba Shugaban Kasar Shawara, Femi Adesina yayi magana da wani dan Jarida Innocent Oweh, a fadar Shugabar Kasar, kan harkar shugabancin Majalisar Kasar, Sojin Kasar wajen fada da Boko Haram, Kasafin Kudin bana, da kuma Yarejeniyar da aka kulla da Kasar Sin (Watau China)

An fara da yi masa tambaya game da matsalar tattalin arzikin da ake ciki. Gami da wannan wasu ma’aikata a Ma’aikatar kudi na Kasar sun yi zanga-zanga game da wasu hakkokin su da ba a ba su ba. Me zaka iya cewa? Na karanta bayanan na su, abin da kenan shine wancan Gwamnati ta soke irin wadannan alawus da suke saba karaba. Sai dai a tuntubi ma’aikatar, su za su fi bada bayani mai gamsarwa.

Ina aka dosa ne a game da tsarin tattalin arziki.

Ana rage barna, gwamnati ba za ta iya cigaba da tafka barnar da aka saba ba. Akwai jerin kayayyaki guda 41 wanda gwamnati ta hana shigo da su cikin Kasa. Muna kashe makudan Kudi wajen shigo da su; Shinkafa, Siminti, Tumaturin gongoni dar da tsinken sakace. Wadannan abubuwa da za mu iya yi da kan mu. A kan wannan tsari ake tafiya.

Majalisar Kasar na zargin ku (Bangaren masu Zaratarwa) da dauki ba dadin da ake ta fama da shi a Majalisar. Me Femi Adesina zai ce kan wannan zargi na su? Kowa na cin gashin kan sa ne, da masu zartarwa, da majalisu da kuma bangaren Shari’a. Ya za ace wani na yi ma wani kutse cikin harkar Sa? Wannan sam ba haka bane. Shugaban Kasa ba zai taba yin katsalandan ba cikin abubuwan da hurumin sa ba.

Shugaba Buhari yayi kokari wajen fadan Boko Haram cikin dan kankanin lokaci. Meye sirrin ne?

Kun dai san Buhari tsohon Janar din Soja ne. Idan kuka duba za ku ga an samu gagarumin canji daga bara zuwa wannan Shekaran. Bari ma, ba za a hada ba. Ya canza Shugabannin gidan Sojin, aka saye kayan aiki, aka kara kintsa su, aka tura su fagen fama. Wannan shi ya kawo mu zuwa inda ake ciki yanzu.

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel