Nigerian news All categories All tags
Real Madrid ta fada ma Manchester United ta zo ga dan wasa

Real Madrid ta fada ma Manchester United ta zo ga dan wasa

– Akwai jita-jitar cewa Dan wasa James Rodriguez na Kungiyar Real Madrid zai koma Kungiyar Manchester United da kwallo.

 – Kulob din Real Madrid na Kasar Spain ta sa ma dan wasan nata kudi.

 – Dan wasan na Real Madrid na so ya koma buga ma Kulob din Manchester United na Ingila.

Real Madrid ta fada ma Manchester United ta zo ga dan wasa

 

 

 

 

Wata Jaridar Birtaniya, Daily Mirror ta rahoto cewa Kungiyar Real Madrid ta sanar da Kungiyar Manchester United cewa dan wasa James Rodriguez na kasuwa. Jaridar ta buga cewa Mai horar da Kungiyar Real Madrid din, Zinedine Zidane a shirye yake da ya saida dan wasan a cikin kakar nan, a kan kudi fam miliyan £50. An samu labarin cewa Dan wasa Rodriguez James har ya saka haya a cikin gidan Sa na Madrid ta Kasar Spain, inda aka ce yana neman wani sabon gida a garin Manchester inda kocin kulob din Jose Mourinho yake da zama a yanzu.

Wani abu shine, dillalin Dan wasan mai shekaru 24 daya ne da na Kocin Kungiyar ta Manchester United, Jose Mourinho. Ana tunanin dillalin na kokarin ganin yiwuwar wannan ciniki. Wasu na ganin rashin kokarin Dan wasan yana da alaka da mai horaswa, Zinedine Zidane. Da alamun cewa Kocin na Real Madrid, Zidane bai yadda da dan wasan na Kasar Colombia ba. A shekarar 2014 ne dai idan ba a manta ba, James Rodriguez din ya koma Kuniyar Real Madrid na Kasar Spain daga Kasar Faransa, inda da yake buga ma Kulob din AS Monaco. A lokacin Kungiyar Real Madrid din ta saye sa kan fam miliyan 60 na dalar ‘EURO’ bayan ya nuna kan sa a gasar cin kofin duniya da aka yi a Kasar Brazil.

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel