Kada Buhari yayi rufarufa akan kisan yan Biafara-Lauyoyi

Kada Buhari yayi rufarufa akan kisan yan Biafara-Lauyoyi

An bukaci Shugaban kasa Muhammadu Buhari da kada yayai watsi da maganan zargin kisan gilla da aka yi wa yan taratsin Biafara a garin Anambra, Imo, Enugu, Delta, Abia,Cross river da kuma Ebonyi, kuma ya kafa wata comitee binciken faruwan. Dubunnan masu zanga zanga ne dai suka yi taho mu gama da jami’an tsaro, wanda yayai sandiyyar mutuwar mutane da dama inda wasu kuma suka jikkata.

Kada Buhari yayi rufarufa akan kisan yan Biafara-Lauyoyi

Masu zangazangra wadanda mambobi ne na kungiyoyin nan masu na masu fafutukar ganin an samar da Kasar Biafara watao IPOB da MASSOB sunyi fitar dango ne a ranar Biafra domin tunawa da tsohon shugaban tarayyyar Bifara wato marigayi Ojukwu.

Suma Yan sandar Najeriya sun bayyan cewa zangazangar ta kazanta har sun yi rashin yan sanda guda 3, tare da kuma wani dan sanda da ake zargin anwurgasa tafkin Niger. Wani mazaunin garin Onitsha mai gani da ido ya fada ma majiyar mu BD SUNDAY cewa a yayin zangazangar, mota 2 na jamian tsrao sun yi arangama da mambobin IPOB lokacin da suke bikin Muranar zagayowar ranar Biafra wanda a dalilin haka mutum 32 suka rasa rayukan su, wasu kuma suka jikkata.

Ya kara da cewa an sojoji sun kama sama da mutum 50 a cikin masu zangzangar, inda suka kais u barikin sojoji na garin Onitsha. Yace “Tarihi ya maimaita kansa a dalilin yadda sojoji suke kasha mutane ba gaira ba dalili. Wannan gwamnatin tana nuna halin ko in kula a yayin da Fulani ke kashe yan Nigeria a duk fadin kasar nan, nayi mamakin yadda sojoji suka harbe mutane a yayin zangazangar lumana, lokaci ne kadai zai tabbatar da ko kasar Nijeria zata shad a irin wannan mugunta” haka majiyar mu wanda bai son a rubuta sunansa soboda gudun rayuwarsa ya fada.

Wani lauya mai kare hakkin dan Adam da ke garin Lagos Ebun-Olu Adegboruwa ya bukaci Babbar kotu da ke Lagos da ta sa a saki mambobin IPOB da gaggawa wadan da gwamnatin tarayya daure su ba akan ka’ida ba. Lauyan wanda ya kasance mai goyon bayan Biafra ne yana tuhumar gwamnati da keta yan cin magoya bayan Biafra, ya kara da cewa kutsawa cikin taron yan IPOB da sojojin kasarnan sukayi da kuma kasha masu zangazanga yi wa sakin layi 39 ne na kundin tsarin mulkin Kasa zagon karan tsaye ne.

Wani lauya da ke lagos Enuwah Omonkaro ya nuna damuwa da irin shirun da Buhari yayi akan batun, ya bada shawarar cewa hanya mafi sauki da Shugaba Buhari zai nunawa Duniya cewa ba zai zura ido ana kasha jama’ar kasar sa ba shine ya kafa wani committee da zai zakulo jami’an tsaron da suka yi wannan aika aika, kuma ya hukunta masu lafi. Y ace “Bai kamata Shugaban kasa yayi shiru ba alhalin wani bangare na kasar suna cikin tashin hankali”

Ya kamata ace Shugaba Buhari ya fahimci cewa shi uba ga dukkan yan Nijeria hard a wadanda basu zabe shi ba. Amma abin haushi har yanzu shugaban yana ganin kamar she shugaban kasan Fulani ne kadai. Garuruwa nawa shugaban ya ziyarta a wannan sashin tun da aka rantsar da shi? Mu fada ma kan mu gaskiya, idan aka banzatar da zargin kashe magoya bayan Biafra masu zangazanga, matsalar zara kara kunno kai a cikin wata mummunar yanayi a nan gaba, amma shugaban kasa yana da dama mai yawa da zai ba marada kunya.

Har way au dai, zargin kisan yan zangazangar Biafra ya cigaba da tabbatar  da kisan gillan da jami’an tsaro suke yi. Ba za’a yarda da wannan abun ba a karkashin mulkin dimokradiya”

 

Kungiyar Amnesty ta bara akan Kisa

Amnesty tayi zargin Sojojin Nijeria da kisan gilla, kuma ta bukaci bincike akan haka, tana cewa binciken da ta gudanar ya tabbatar mata da cewa Jami’an tsaro sun harbe yan-baruwana a yayin zangazanga magoya bayan Biafra a garin Onitsha, Anambra. Kamar yadda MK Ibrahim ya fada, Shugaban Amnesty in ternational a Nijeriya yace hujjojin da aka samo daga masu gani da ido, Asibitoci da kuma wurin ajiye gawa sun tabbatar da Sojoi sun bude wuta akan yan IPOB, magoya bayansu day an ba ruwana a wurare 3 a cikin garin a tsaknin 29 zuwa 30 ga watan mayu. “Bude wuta akan masu zangazangar lumana magoya bayan IPOB wadanda ba su yi barazana ga kowa ba tamkar yin amfani da karfi iko ne wanda hakan yayi sandiyyar mutuwar mutane da dama”.

 

A wani faruwan, mutum 1 ya rasa ransa bayan Jami’an tsaro sun far musu a lokacin da yake barci. Ba’a san Tabbataccen kididigan mutanen da suka rasu ba sobada sojoji ssun yi awon gaba da wasu gawawwaki da kuma wadanda suka jikkata. “wannan ba shine karon farko bad a magoya bayan IPOB suska mutu a hannun Sojoji ba. Hakan na damun mu, kuma ya kamata a bincike wannan lamarin. Bugu da kari, dole a kawo karshen wannan irin tura Sojoji yin aikin yan sanda” In ji shi. Ya karfafa maganan harbin akan kisan gilla kuma dole a yi gaggawan bincike tare da tabbatr da yi wa masu hannu a cikin lamarin hukunci.

 

Cin gashi kan Kananan hukumomi ma zai yi maganin matsalar-Ted Iseghohi-Edwards

Shugaba da kuma sakatare na hadaddiyar kungiyar kananan Hukumomi na Nijeriya ya ba Gwamnatin tarayya shawara da ta binciki zargin kisan da aka yi, ya kara da cewa ba I kamata a rika lamuntar Jami’an tsaro su bude wuta akan masu zangazangar lumana. “Ya kamata Gwamnati ta tabbatar da sahihancin kisan. Zai iya yiwuwa akwai sa hannun miyagun mutane a cikin lamarin, suka yi amfani da zangazangar suka haifar da tashin tashina wanda yayi dalilin Sojoji suke bude wuta. Idan bah aka ba, kisan wanda bai jib a bai gani ba, ba a bin ayi maraba das hi bane. Duk wanda da sa hannunsa a ciki, a kama shi. Mai yiwuwa ne wadanda sukayi harbin, sun yi hakan ne ba tare da an basu izini ba, amma idan Shuwagabannin Sojojin ne suka basu izinin su kasha mutanen da babu ruwansu, to a zakulo su kuma a hukunta su.” Ya fada ma BD SUNDAY a wata hirar da suka yi.

 

An tambayeshi ko zai Kawo hanyoyin da Shugaban Kasa zata bi ta magance matsalar sai yace, karfafa cin gashin kan kananan Hukumomi domin taimaka ma talaka a Nijeriya zai kawo sauki sosai ga magance matsalar masu taratsi da kuma ta’addanci a Kasar nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel