Kwallon Cristiano Ronaldo tafi kyau a Champions league

Kwallon Cristiano Ronaldo tafi kyau a Champions league

– An zabi kwallon Cristano Ronaldo a matsayin wanda ya fi kowane kyau a gasar Zakarun Nahiyar Turai na shekarar banan 2015/16.

 – Dan wasan na Kungiyar Real Madrid ya ci kwallon ne a wasan su da Kungiyar AS Roma ta kasar Italiya a zagaye na biyu.

 – Kyaftin din Kasar ta Portugal ya jefa kwallaye 16 a gasar wasan bana, inda Kungiyar Real Madrid din tasa ta dauki kofin karo na goma sha daya.

 

Kwallon Cristiano Ronaldo tafi kyau a Champions league

 

 

 

 

 

 

An zabi kwallon da Cristiano Ronaldo yaci AS Roma a gasar kofin turai na ‘Uefa Champions league’ a matsayin mafi kyau a shekaran nan.

Dan wasan gaban na Real Madrid ya samu kaso 36% na kuri’un da aka kada a shafin yanan gizon Kungiyar Kwallon Kafar ta Turai watau UEFA. An dai zabi kwallon Ronaldo sama da na Saul Niguez, wanda ya ci Kungiyar Bayern Munchen da kuma wanda Alessandro Florenzi ya ci Kungiyar Barcelona tun daga kan tsakiyar layi.

Cristiano Ronaldon yaci kwallon ne bayan ya zuro a guje ta layin hagu, ya kuma yanke dan wasa Florenzi na Roma, sai ya karkato ya caki kwallon da karfin tsiya, kamar yadda ya saba da badamiyar kafar sa, sai ga kwallo a can saman zaren AS Roma na lilo daga banagaren dama. Kungiyar ta Real Madrid dai tayi nasara a wasan da ci 2-0, inda Jese Rodriguez ya jefa kwallon Sa yayin da aka kusa tashi bayan ya jawo ta tun daga nesa. A zagaye na biyun wasan haka Real Madrid din ta kara doke Kungiyar AS Roma da ci 2-0, haka dai suka je har suka ci Kungiyar Atletico Madrid a wasan karshe, inda dai shi dan wasa Ronaldo din ya ci bugun finaritin (bugun daga kai-sai mai tsaron gida) karshe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel