Amurka ta tuhumi ‘yan majalisa kan abin kunyar lalata

Amurka ta tuhumi ‘yan majalisa kan abin kunyar lalata

-Tsugunne ba ta kare ba dangane da batun lalata na ‘yan majalisar wakilai a Amurka

-Shaidu na nuna cewa ‘yan majalisun tarayyar da suka yi abin kunyar neman yin lalata a Amurka an yi musu tambayoyi a can

-Wadanda ake zargi sun yi barazanar kai Amurka kara

 Wani rahoto da jaridar This Day ta buga na cewa, jami’an ma’aikatar kula da harkokin kasashen waje ta Amurka, ta yi wa ‘yan majalisar nan 10 da suka je Cleveland da ke jihar Ohio a Amurka ziyarar aiki, tambayoyi dangane da neman yin lalata wanda 3 daga cikin abokan tafiyarsu suka yi a can.

Amurka ta tuhumi ‘yan majalisa kan abin kunyar lalata
Jakadan Amurka a Nigeria, James Entwisl

Jakadan Amurka a Najeria James Entwisle ne ya zargi  ‘yan majalisar su uku Mark Gbillah da Samuel Ikon and Gololo da neman yin lalata da matan banza a yayin ziyararsu kasar, hakan na kunshe ne a wata takardar koke da ya aikawa Kakakin majalisar  Yakubu Dogara.

Ana zargin cewa ‘yan majalisar sun yi yunkurin yi wa wata ‘yar aikin otal din da suka sauka fyade, yayin da sauran suka nemi yin lalata da matan banza.

KU KARANTA: Za’a saurari ra’ayin mutane kan lalatar yan majalisa

Cikin tawagar da aka yi tafiyar da su zuwa Amurkan sun hada mataimakin shugaban kwamitin hulda da manema labarai Jonathan Gaza Gbewfi da shugaban kwamitin hulda da kasashen waje Rita Orji, sannan da Ayo Omidiran da Nkole Ndukwe da kuma Danburam Abubakar.

‘Yan majalisar uku sun musanta zargin, sun kuma yi barazanar kai karar gwanatin Amurka kan batun. Kakakin majalisar shi ma, ya bukaci Amurka da ta kawo kwakkwarar shaida kan zargin.   

Asali: Legit.ng

Online view pixel