EFCC ta gano manyan gidaje 3 dake da alaka da Fayose

EFCC ta gano manyan gidaje 3 dake da alaka da Fayose

-Matsalolin Gwamna Ayodele Fayose na dada tsauri, yayin da hukumar EFCC ta gano hanyar da ya kasha wasu kaso daga cikin kudaden da ya karba daga asusun ONSA

-Gidaje uku na da nasaba da abokanan tarayyan Fayose, wanda ake ganin suna shige masa gaba

-Hukumar ta ce zata duba yiwuwar kame kaddarorin a karkashin  Hukumar EFCC

EFCC ta gano manyan gidaje 3 dake da alaka da Fayose
EFCC logo

Jaridar The Nation ta ba da rahoto cewa Hukumar yaki da cin hanci da rashawa wato EFCC ta gano manyan gidaje uku na wani mafi kusanci ga Gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose. Fayose na fuskantar kalubale biyu, yana karkashin binciken hukumar EFCC kan karban kudade daga ofishin tsohon mai ba shugaban kasa shawara a harkan tsaro, a lokacin gwamnatin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

KU KARANTA KUMA: Bani da matsala da Ali Modu Sheriff- Makarfi

Yana kuma fafatawa da matar shugaban kasa, Aisha Buhari a kan zargin da yake yi akanta cewa ta taimaka a cikin satar wasu kudade na Haliburton. A sabon rahoto da aka samu, daya daga cikin gidajen na babban birnin tarayya Abuja, yayinda sauran biyun ke jihar Legas, kuma anyi imanin cewa an siya gidajen ne daga cikin naira biliyan N1.219 da Fayose ya karba a lokacin zaben sa na gwamna a jihar sa.

Fayose ya karyata zargin ya kuma kira sunan sarsalar da ta dauki nauyin kudaden zaben. An ce hukumar na iya kwace kaddarorin karkashin ikon ta, tunda an samu nasaba tsakanin naira biliyan N1.29 da ake zargin Fayose da kuma gidaje uku.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel