Buhari ya naga sabon shugaban ma'aikatar 'Inland waterways'

Buhari ya naga sabon shugaban ma'aikatar 'Inland waterways'

Shugaba Buhari ya amince da nadin Boss Gida Mustapha a matsayin shugaban ma'aikata mai kula da ruwa da kogunan cikin kasa watau National Inland Waterways Authority kamar dai yadda jaridar Leadership ta ruwaito.

Buhari ya naga sabon shugaban ma'aikatar 'Inland waterways'

Wannan yana kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin tarayya ya fitar. Sanarwar tace nadin na tsawon shekara 4 ne. Wannan nadin dai yana nufin sabon shugaban zai anshi ragamar hukumar daga hannu Danladi Ibrahim wannan yake rike da ita na wucin-gadi tun watan June shekar da ta gabata.

Shi dai Mustapha lauya ne wanda kuma yake da kwarewa sosai wurin harkar gudanarwa kasuwa da aikin gwamnati. Mustapha dan jihar Adamawa ne kuma ya taba rike matsayin mataimakin shugaba na kasa a jam'iyyar ACN wadda daga baya ta rikide ta koma APC.

Ku karanta: Aisha Buhari ta ba Fayose kwana 5 ya janye zarginsa a kanta

Mustapha din kuma ya taba shugabantar kwamitin mutane 7 da suka tantance mutane 27 masu neman tsayawa takarar gwamnan jihar Kogi a zaben da ya gabata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel