Barcelona na neman dan wasa daga Mancity da Chelsea

Barcelona na neman dan wasa daga Mancity da Chelsea

Wata jaridar kwallon kafa mai suna Voetbal ta ruwaito cewa mai yiwuwa kulob din Barcelona ya maye gurbin Neymar da Kevin De Bruyne da Eden Hazard.

Barcelona na neman dan wasa daga Mancity da Chelsea
Barelona

Jaridar ta ruwaito cewa ManUtd da RealMadrid suna jawarjin dan kasar Brazil din kuma ma har Barcelona sun fara shire-shiren tafiyar tasa. Majiyar tamu har wa yau ta ce kulob din yana kuma duba yiwuwar siyen dan wasan Juventus Paulo Dybala, Griezmann na Atletico da kuma Costa na Bayen.

Ku karanta: Vardy ya ki yadda da tayin Arsenal

Shidai Neymar din an kayyade kudin barin sa kulob din da kudi masu yawan da suka kai €190m. Wakilin dan kwallon kuma Wagner Ribeiro ya bayyana cewa Neymar din yana jin dadin Barcelona amma kuma wasu kungiyoyin na neman sa wadan da kuma suke na niyyar biyan sa makudan kudade. Kungiyoyin sun hada da Real, PSG da kuma ManU.

"Kuyi hakuri ban iya fada muku fiye da haka a yanzu saboda maganar sirri ce. Maganar da zan iya fada muku dai itace Neymar yana jin dadin buga wasa a Barcelona" inji wakilin na sa.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel