Yadda fadan sojoji da yan sanda ya kaya

Yadda fadan sojoji da yan sanda ya kaya

Sojoji da yan sandan Najeriya sun fito sun bayyana yadda fada ya barke a tsakanin su a gidan gwamnatin jihar Borno jiya Alhamis 23 ga watan nan wanda kuma yayi sanadiyyar jima wani dan sanda rauni.

Yadda fadan sojoji da yan sanda ya kaya
Sojojin Najeriya

Kamar dai yadda suka shaida a cikin wata takardar da suka fitar ta hadin gwuiwa tsakanin runduna ta 7 da sojoji da kuma kwamishinan yan sandan jihar tace wani dan sanda ya samu raurin harsashe sakamakon fadan. Rahotannin da suka fara fita jiyan dai sun bayyana cewa sojoji ne suka fusata sakamakon yan sanda da suka hana su shiga gidan gwamnatin jihar inda ake raba kayan abinci.

Daga nan sai sojojin suka bude ma yan sandan wuta. Daga bisani suma yan sandan sai suka farma sojojin inda suka lakadawa wani daga cikin su duka.

Ku karanta: Aisha Buhari ta ba Fayose kwana 5 ya janye zarginsa a kanta

A cikin sanarwar hadin gwuiwar da suka fitar duka bangarorin biyu sunyi Allah-wadai da halayyar ja'iyan nasu sannan kuma suka sha alwashin bincika lamarin dakuma kukunta duk wanda aka samu da laifi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel