Yan Hisbah Na hukunta marasa Azumi a Jihar Kano

Yan Hisbah Na hukunta marasa Azumi a Jihar Kano

-Watan azumin Ramadan wata ne da musulumai ke dauka da muhimmanci

-Wata ne mai tsarki, ana bukatan ko wane mabiyi addinin islama ya yi azumi kuma ya kama kansa.

-Sojojin addinin islama a Jihar Kano suna tabbatar da cewa musulmai sun bi umurnin Allah a cikin wata mai albarkan.

 

Yan Hisbah Na hukunta marasa Azumi a Jihar Kano
yan hisbah

 

Game da wata Rahoton daga Jaridar herald, duk wanda aka kama ba ya azumi, sai ya sha bulala a gaban jama'an unguwar su. Kungiyar hisbah tuni ta kama mutane da dama da suka ki bin umurnin Allah na yin azumi a cikin watan Ramadan, kuma hisbah na kokarin tabbatar da cewa an yi azumi.

Rahoton ta hararo cewa tun farkon watam Ramadan, hukumar hisbah na ankare da wurare da dama da ta san akan saba umurnin Allah domin neman masu laifi cikin watan Ramadan. .idan aka kama mutum, zai sha tambayoyi kala kala, kuma idan bai da uzuri gamsashe, za'a gurfanar da shi,a yankw mai hukunci kuma a azabtar da shi a bisa doka.

, muna daure su a ofishin hisbah na tsawon makonni 2 akalla domin ilmantar da su muhimmancin azumi,  muna kan batun mu na cewa sai mun yi iya kokarin ganin sai kowa yayi azumi a jihar kano. Muna da karan mutanen da suka ki yin azumi a wannan watan, sanoda haka, za mu tura mazan mu su kamo su. Nabahani usman,Mataimakin kommandan hisban jihar kano yace .

A gefe daya, gwamnatin jihar kebbi ta karyata rahoton kafafan yada labarai na mutuwan yarinya yar shekaru 5 a jihar a sakamakon turmutsutsin karban abincin , a shirin ciyarwan watan ramadanan da matar Shugaban kasa, Aisha buhari ta shirya.

KU KARANTA: Ku karanta dalilin hukumar Hisbah ta jihar Kano kama mata guda 31

Matar gwamnan jihar kebbi , dr. Zainab atiku ta fada wa manema labaran Legit.ng cewa karya ne , babu alamun gaskiya a ciki.

Ta ce yarinyar da iyayen ta ba su a wurin ma lokacin da abun ya faru. Kuma ba wani abu ya faru ba illa wani dan hargitsin da bai taka kara ya karya ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel