Babban hafsan sojin sama ya gurfana a gaban kotu (hotuna)

Babban hafsan sojin sama ya gurfana a gaban kotu (hotuna)

-Wani babban hafsan sojin sama mai mukamin Air Vice Marshall ya gurfana a gaban kotu

-Hafsan sojin ya bayyana ne a cikin kayan sarki

-EFCC ta jaddada matsayinta na ba sani, ba sabo a yaki da cin hanci rashawa  

Air vice Marshal Ojuawo, wani babban hafsan rundunar sojin sama, ya gurfana a gaban wata babbar kotu a ranar Alhamis 23 ga watan Yuni a cikakkiyar shiga ta kayan sarki irin na rundunar.

Babban hafsan sojin sama ya gurfana a gaban kotu (hotuna)
Air Vice Marshal Ojuawo wanda EFCC ta gurfanar

Hukumar yaki da yi wa tattalin arzikin zagon kasa EFCC, ce ke tuhumar hafsan da hannu a badakalar dala biliyan 2 da miliyan 1 na sayen makamai, hafsan ya gurafana ne a gaban wata babbar kotu birnin tarayya Abuja.

Babban hafsan sojin sama ya gurfana a gaban kotu (hotuna)
Air Vice Marshal Ojuawo a harabar kotun a kayan sarki na rundunar sojin sama tare da jami'an EFCC

A wasu hotuna da hukumar EFCC ta lika a shafinta na dandalin muhawara da sada zumunta na Facebook, ta na mai cewa. “ku dubi wadannan hotuna na wani babban hafsan rundunar sojin sama ne mai mukamin Air Vice Marshal Ojuawo, wanda ya gurfana a gaban babbar kotu  birnin tarayya da ke zama a Apo, a Abuja bisa tuhumarsa da laifin almundahana. Ya kuma zo kotun ne a cikin shigar kayan sarki…”

Babban hafsan sojin sama ya gurfana a gaban kotu (hotuna)
Air Vice Marshal Ojuawo a cikin kotun       

KU KARANTA: EFCC na shirin gayyatar matar Fayose kan kudin makamai

Sanarawar hukumar a shafin tauna aya ne, ma'ana gargadi da ke nuni da cewa kuma kamar yadda ta fada, ba sani ba sabo aikinta, kuma za ta bayar da cikakken bayani game da shari'ar nan gaba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel