Ba yarinyar da ta mutu a Kebbi - Dr. Zainab Bagudu

Ba yarinyar da ta mutu a Kebbi - Dr. Zainab Bagudu

- Shirin ciyarwan  watan Ramadana , wanda matar Shugaban kasa , hajiya  Aisha Muhammad Buhari , ta kaddamar na cigaba da gudana

 -An bada rahoton cewa wata yar shekara 5 ta mutu a cikin  turmutsun amsan abinci.

Ba yarinyar da ta mutu a Kebbi - Dr. Zainab Bagudu
aisha da iyayenta

Gwamnatin Jihar Kebbi ta karyata rahoton tashoshin yada labarai na cewa wata yar shekara 5 ta rasa ranta a sakamakon turmutsin amsan abincin a shirin ciyarwan watan Ramadana da matar Shugaban Kasa, Hajia Aisha Buhari ta kaddamar.

Jaridar Leadership ta bada rahoton cewa wata yarinya ta mutu a cikin ma'ikatar kula da harkokin da ya shafi mata na Jihar Kebbi wurin rabon abinci. Rahoton ta shaida cewan Mahaifiyar yarinyan mai suna Aisha ta amsa buhun shinkafa mai kilo 25 , yayinda take fita daga cikin ma'aikatan, sai mutane suka rufe ta.

Matar Shugaban karamar hukumar Bunza a Jihar Kebbi, Hajiya Fadima Muhammad Bunza ta wakilce matar gwamnan Jihar Kebbi, Dakta Zainab Atiku Bagudu. Yayinda ta ke ba manema labaran Legit.ng jawabi, ta karyata rahoton da ke cewa an kashe yarinya. Ta ce karyne , yarinyan da Mahaifiyar ta ba su a wurin da aka samu hatsaniya. Hatsaniyan ma kawai dan rashin jituwa ne da bai taka kara ya karya ba.

KU KARANTA: Kebbi ta zo ta 2 a kiwo, za kuma ta hada hannu da Lagos

Ku tuna cewan gwamnatin Jihar kebbi na cikin yunkurin samar da shinkafa ga mutanen jihar, a kwanankin baya ta hada kai da gwamnatin jihar legas domin samun cigaba a kan harkan noma musamman noman shinkafa a jihohin guda biyu.

A gefe daya kuma,matar shugaban kasa Hajiya Aisha Muhammadu Buhari ta mayar da martani wa gwamnan Jihar Ekiti, Ayodele Fayose da cewa “ Fayose mahaukacin kare  na”

Asali: Legit.ng

Online view pixel