Jam'iyyar PDP na harin Buhari, APC kan Fayose

Jam'iyyar PDP na harin Buhari, APC kan Fayose

-Jam’iyyar PDP sun bayyana daskarar da asusun Fayose na da nasaba da siyasa

-Jam'iyyar PDP sun bukaci cewa jam’iyya me ci dole ne ta dakatar da mayyar-farauta domin neman zaman lafiya da kwanciyar hankalin kasar.

-Fayose ya fallasa rawar da Aisha Buhari ta taka a cikin cin hancin Jefferson

Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta bayyana daskarar da asusun Fayose a matsayin wanda ke da nasaba da siyasa.

Jam’iyyar ta PDP bukaci cewa lallai jam’iyya mai ci ta dakatar da mayyar-farauta da take yi domin neman zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar.

Jam'iyyar PDP na harin Buhari, APC kan Fayose

Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da shugaban kwamitin masu talla, Mr. Dayo Adeyeye yayi.  Jam’iyyar ta bayyana daskarar da asusun Fayose a matsayin ba bisa doka ba, rashin yanci, da kuma zalunci.

KU KARANTA KUMA: Obanikoro, Fayose sun ci sama da naira biliyan N4.745

Jam’iyyar ta yi Allah wadai da daskarar da asusun Fayose, ta kuma ce hukumar EFCC ta saki asusun nan da nan, cewa aikin keta sashe na 308 a cikin kundin tsarin mulki na shekara ta 1999, a matsayin gwamna mai ci, ba zai iya tsayawa ko wace fitina ba har sai ya sauka daga kan kujerar mulki.

An ce an biya kudi mai yawa N1,219, 490,000 cikin asusun Fayose da kuma asusun kamfani, wanda ya hada da miliyan N100, wanda aka biya cikin asusun Spotless Investment Limited.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel