Petr Cech ya kafa mummunan tarihi a gasar EURO 2016

Petr Cech ya kafa mummunan tarihi a gasar EURO 2016

- Petr Cech ya kafa mummunan tarihi a gasar EURO.

 – Gola Petr Cech ya bar mummunan tarihi a gasar kwallon kafar EURO2016.

 – Kasar Turkiyya ta ba Kasar Czech Republic kashi.

 – An samu dura wa mai tsare ragar kwallaye 21, a fadin gasar nahiyar Turai.

 

Petr Cech ya kafa mummunan tarihi a gasar EURO 2016

 

 

 

 

Mai tsaron ragar kasar Czech Republic, Petr Cech ya kara shan wasu kwallaye 2 a karawar su da Kasar Turkiyya. Inda dan wasan mai tsare gida ya bar tarihi a gasar. An koro kasar Czech Republic din gida daga gasar ta EURO inda dan wasan Kungiyar Arsenal din ya kafa wani mummunan tarihi.

Burak Yilmaz da kuma Ozan Tufan suka zuba ma Kasar Turkiyyan kwallaye a wasan su da Kasar Czech Republic wanda aka tashi da ci 2-0. Wannan ya nuna cewa Petr Cech din ya bar tarihi a gasar na zakarun nahiyar kwallon kafan Turai, inda aka dura masa kwallaye a ragar sa daya-daya har guda 21. A kaf tarihin gasar a duniya, ba a taba samun wanda aka zura ma kwallo kamar sa ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel