AS Roma ta saye wasu ‘yan wasan Najeriya

AS Roma ta saye wasu ‘yan wasan Najeriya

- Kungiyar Kwallon AS Roma ta saye wasu ‘yan wasan Najeriya.

 – Kulob din AS Roma sun saye wasu ‘yan Najeriya 2.

 – ‘Yan wasan sun buga wasa ne a kulob din Spezia, a gasar shekarar nan da ta gabata.

 – Kulob din AS Roman sun kuma saye dan wasan AC Milan Stephan El Shaarawy a kan fam miliyan €13.

AS Roma ta saye wasu ‘yan wasan Najeriya

 

 

 

 

 

Kungiyar wasan kwallon kafar kasar Italiya ta AS Roma, ta saye wasu matasan ‘yan wasan Najeriya Sadiq Umar da Nura Abdullahi. Umar Sadiq dai yaci ma Kungiyar ta Roma kwallaye 2 cikin wasanni 6 da ya samu ya buga a bana. An saye tsofaffin ‘yan wasan na Abuja Football College stars ne a kan farashi fam miliyan 5 na dalar euro. Sun kuma sa hannu kan yarjejeniyar shekaru 4 da kungiyar ta Roma.

‘Yan wasan sun buga wasa ne a kulob din ‘Spezia’, a gasar shekarar 2015/2016 da ta gabata. Amma yanzu sun dawo kulob din AS Roma da taka leda kan farashi fam miliyan €2.5 kowannen su. Kungiyar ta Italiya ta tabbatar da sayen ‘yan wasan ta ta shafin ta na twitter @ASRomaEN, a ranar 21 ga wannan wata, inda ta ke cewa Sadiq Umar da Abdullahi Nura sun zama ‘yan wasan mu yanzu:

Kungiyar AS Roma kuma ta kammala cinikin dan wasan gaban nan El Shaarawy, daga kulob din AC Milan kan kudi fam miliyan 13 na dalar Euro. Dan wasan mai shekaru 23, ya rattaba hannu kan kwantiragin shekaru 4 shima, bayan ya kammala wata 6 a matsayin dan wasan aro a kulob din Romar a gasar shekarar 2015/16.

Asali: Legit.ng

Online view pixel