Ba Yarjejeniyar tsaigaita wuta da Gwamnati - Tsagerun NDA

Ba Yarjejeniyar tsaigaita wuta da Gwamnati - Tsagerun NDA

-   Tsagerun Neja Delta sun karyata jita jitar yarjejeniyar tsaigaita wuta da gwamnatin tarayya.

-   Tsagerun Neja Deltan sun ce hedkwata su ba tada masaniya bisa wani tsagaita wuta.

Kungiyar yan bindiga, Tsagerun neja delta ya karyata shiga wani yarjejeniyar tsagaita wuta gwamnatin shugaban kasa Muhammadu buhari.  A sanarwan da ta bada ta shafinta a Twitter,kungiyar tsagerun neja deltan tace hedkwatar su ba tada masaniyar yin hakan.

 “Hedkwatan NDA ba ta shiga wani yarjejeniyar tsagaita wuta da gwamnatin najeriya batace.

Ba Yarjejeniyar tsaigaita wuta da Gwamnati - Tsagerun NDA
tsagerun neja deta

Duk da haka , Dakta Muhammad Barkindo yayi kira ga gwamnatin Najeriya da ta bi sannu sannu wurin kawo karshen ayyukan yan bindigan. Dr. Muhammad Barkindo, wanda tsohon direkta manaja ne a kamfanin man Najeriya NNPC ya fada wa manema labaran fadar Shugaban kasa jim kadan bayan ganawarsa da Shugaba Muhammad Buhari a fadar Shugaban kasa, a babban birnin tarayya Abuja. Yace

“Ni a gani na, bin sannu sannu ne kawai zai kawo ci gaba. Na san gwamnati na zaman sulhu a yanzu kuma an fara samun sakamako mai kyau. Saboda haka kada muyi gaggawa. Amma ina da yakinin cewa ta wannan yarjejeniyar,  za'a samu sakamako mai kyau saboda yankin neja yankin neja delta na da muhimmanci ga kasan nan.

KU KARANTA: Gwamnatin, tsagerun Neja Delta sun cimma yarjejeniyar

Tsagerun neja delta ta dau alhakin sanya wa kafufuwan mai a yankin neja bama bamai a kwanakin bayan. Hakazalika , Tsagerun neja delta sun karyata cewa sun gana da ministan mai , ibe kachikwu. Sun ce duk wanda yace ya gana da gwamnati, ba wakilin su bane.

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel