Dokar Hana Addini ta Sabawa kundin tsarin mulki – Osinbajo

Dokar Hana Addini ta Sabawa kundin tsarin mulki – Osinbajo

-'Yancin fada aji, ba 'yanci bane mai mahummanci kawai ba, hanya ce ta cima wasu 'yantuttikan.

 

Dokar Hana Addini ta Sabawa kundin tsarin mulki – Osinbajo

Mataimakin shugaban kasa ya fada cewa duk wani kokari na yi ma 'yancin yin ibada tarnaki bashi bisa ga doka. Jaridar Sun ta ruwaito cewa mataimakin shugaban kasar yayi wannan jawabi a wani taro na masana shari'a a Abuja ranar Litinin, 20 Yuni, 2026 inda ya ce duk wani kokarin hana 'yancin yin ibada, yayi ma doka karan tsaye.

Mataimakin shugaban kasar wanda shaihin malamin shari'a ne yayi wannan jawabi ne a wani taro na kwana daya mai suna "Mahadar addini da  doka: A idon duniya" Osinbajo ya cigaba da cewa "duk kasar da bata da addinin ta amma ta bada 'yancin yin ibada zata zama kasa Mai zaman lafiya da walwala"

Za'a iya tunawa cewa gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya Sha suka game da doka da ke gaban majalisar dokokin jihar wadda zata takaice maganar wa'azi a cikin jihar.

KU KARANTA: Aregbesola ya fito yayi magana akan Hijabi

Mabiya addinin krista suna ba gwamnan shawara da ya janye dokar. Sun lashi takobin ganin cewa ba'a sama mabiya addinin krista wani tarnaki ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel