Musa yaron da kishiya ta sabauta ya murmure

Musa yaron da kishiya ta sabauta ya murmure

Musa yaron da ake zargin kishiyar uwa da yi wa aika-aika a Kano ya murmure, ana kuma shirin sallamarsa daga asibiti.

Aisha, uwargidan shugaban kasa Muhammadu Buhari ta aika da hotunan Musa. Uwargidan shugaban Najeriya ce tasa aka dauko Musa daga Kano zuwa wani asibiti a Abuja domin ya samu kyakkyawar kulawa. A cewar  Aisha Buhari .“Likitoci sun ce zai warke amma sai dai ya samu nakasa saboda mugunta da aka yi masa ta wuce misali. Don haka ina kira ga gwamnatin Kano da tabbatar da cewa an hukunta wanda suka aikata wannan aika-aika. Yara sune manaya gobe, don haka dole mu mu kula da su.

KU KARANTA: Wani ya kashe matar sa saboda N100

Musa yaron da kishiya ta sabauta ya murmure
Musa a asibiti yayin da Sarki Kano ya je ziyara

A na zargin karkar Musa, Hafsatu da kishiyar babarsa Zainab da hadin baki a kauyen Gulu da ke karamar hukumar Rimin Gado ta jihar Kano, da yanke mi shi harshe, da soke masa idonsa na dama, da kuma marainansa ta hanyar amfani da abu mai kaifi, kasancewar mahaifiyarsa ba ta gidan, sakamakon sabanin da ta samu da mahaifin yaron wanda hakan ya kai ga mutuwar auren.

Wanda hakan ya sa aka bar Musa da ‘yar uwarsa a hannun kakarsa ta wurin uba, da kuma kishiyar uwa wadanda ake zargin su da yi wa Musa lahani.

Musa yaron da kishiya ta sabauta ya murmure
Musa ya na murmurewa a wani asibiti a Abuja

 A yayin da Sarkin Kano Muhammadu Sunusi ya ziyarci yaron a asibiti, ya yi kira da a hukunta wadanda suka aikata wannan danyen aiki. Mahifiyar yaron Zainab ta bukaci da a dawo mata da ‘yar ta gudun kar ita ma a yi mata irin na Musa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel