Olamfics 2016: Rashin shiri managarci zai jawo tsaiko

Olamfics 2016: Rashin shiri managarci zai jawo tsaiko

Kamar dai yadda masu iya magana suke cewa 'ba'a fafa gora ranar tafiya'. Yanzu dai saura kimanin wata biyu kacal a fara garsa Olamfics a Rio de Janeiro dake kasar Brazil amma tawagar kasar Najeriya bata yi wani shin azo-a-gani ba dan gane da gasar. Wannan nema ya sa wasu yan kasar shakku anya kuwa kasar zata iya yin wani katabus a gasar.

Olamfics 2016: Rashin shiri managarci zai jawo tsaiko

An dai fara samun tsaiko ne tun daga wajen takaddamar bajet din kasar inda duka-duka sai satin da ya wuce ne ma aka sa hannu wajen fitar kudin da za'ayi anfani dasu.

Wata matsalar kuma da ta kunno kai shine yadda ake ta samun matsala wajen fitar da kudin da za'ayi ma yan wasan 'biza' don zuwa gasar. Duk da kuma kiraye kirayen da masu ruwa-da-tsaki a harkar sukeyi a kan ayi gyara abun ya citura. Wata wadda ta lashe gasar tsere a shekarun baya ma dai Mary Onyali ta bayyana fargabar ta wajen rashin shiri kwakkwaran da tawagar Najeriyar bata yi ba.

An ruwaito cewa ta bayyanama kamfanin dillacin labarai na kasar nan cewa: "Ina cike da fargabar cewa kasar nan bazata tabuka komai ba. Ba wai fata nike ba amma ai alamar karfi tana ga mai kiba. Idan bamuyi shiri mai kyau ba ta ya za'ayi mu samu nasara? A yayin da sauran kasashe ke maida hankali wajen shire-shire mu kasar nan addu'a kawai muke yi."

Shima dai wani shahararren dan kwallon tebur na kasar Segun Toriola ya bayyana ma kamfanin dillacin labaran kasar nan cewa: "Ina tunanin wannan karon kam Najeriya sam bata shirya ba. Abun ma duk yafi na baya muni domin har yanzu ba'a fara komai ba.

"Ina tunanin kar ma wani dan kasar nan ya sa ran za'a samo wata lambar yabo domin lokacin da wasu kasashen suka kammala shire-shiren su mu nan ko fara wa ma ba'a yi ba".

Shi ma dai ministan matasa da wasanni Solomon Dalung ya bayyana rashin jin dadin sa game da yadda abubuwar suka tabarbare a kasar a wannan shekarar yayin da yasa alwashin zai yi duk abun da ya dace don ganin an kammala shire-shiren cikin lokaci.

"Zamu fara shirin atisaye wanda muka tsara shi gida biyu. Za'a fara yin shiri na farko a cikin kasar nan sannan kuma ayi dayan a wajen kasar saboda rashin kayan aiki isassu." Ina kuma kara kira ga yan wasan da su maida hankali suyi kokari sosai don kuwa dai duka kasar nan akeyi ma aiki kuma martabar kasar nan muke so mu daga. Ina kuma tabbarat muku da cewa zamu samu nasa" inji ministan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel