Wani ya kashe matar sa saboda N100

Wani ya kashe matar sa saboda N100

Jaridara Vanguard ta ruwaito wani Onekachi Anele dan shekara 36 ya fari matar sa Chikodi wanda yayi sandiyyar mutuwar ta har lahira saboda N100. Yanzu haka dai yana hannun 'yan sanda a kulle.

Wani ya kashe matar sa saboda N100

Sifeton Yan sanda

An ruwaito cewa miji da matar sun samu sabani ne inda mijin ya mari matar ita kuma ta rama sai shi kuma gaura mata wani marin wanda yayi sanadiyyar mutuwar matar tasa. Su dai ma'auratan mazauna unguwar Obiniezena a garin Owerri ta arewa kafin faruwar lamarin.

Kwamisinan yan sandan jihar Taiwo Lakanu ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya bayyana cewar tuni yan sanda sun fara binciken lamarin. Shi ma dai mijin ya bayyana cewa: "Matar zagi na tayi ni kuma da naji haushi sai na mare ta amma sai ta rama. Ni kuma sai na harzuka na shara mata wani marin inda har ta suma daga baya kuma ta mutu."

Sai dai kuma mijin ya nuna nadamar aikata hakan inda yace yana son matar sa sosai kuma bai mare ta ba don ya kashe ta. Mijin ya kara da cewa: "Ina son mata ta sosai, babu yadda za'ayi in kashe ta. Kawai dai yar matsala aka samu da har ta jawo mukayi mare-mare da ita."

Ya kuma cigaba da kewa sun haifi 'ya'ya biyu da matar tasa mace da namiji.

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel