Yadda yan bindiga suka kasha mijina- Mrs Buhari

Yadda yan bindiga suka kasha mijina- Mrs Buhari

-   Mrs Ramota Buhari ta yi bayanin yadda yan bindiga suka kashe mijinta a Jihar Ogun.

-   Tace sun harbe yarinta yar shekara 13.

-   Jami'an yan sanda kimanin yan bindiga 100 suka zo.

-   Har yanzu bincike na kan gudana.

Mrs Ramota Buhari ta bayyana yadda aka yi wa mijinta, Waheed Buhari, kisan gilla. Ta ce yan bindigan sun mamaye unguwar Imushin dake Ogijo, karamar hukumar Sagamu a karshen makon nan.

Yadda yan bindiga suka kasha mijina- Mrs Buhari
yan bindiga

Jaridar New Telegraph ta bada rahoton cewa yan bindigan sun zo ramuwar gaya ne. Mrs Ramota tace sun harbi yarinyarta yar shekara 13 a yayin kawo harin.Ramota tace an harbe mijinta ne jim kadan bayan ya zaga bayan gida domin kama ruwa.

Tace:

“Ina rike da shi, ina kuwan a zo a taimake ni sai aka ce min an harbi yarinya ta. Dakin mu muna bacci kafin karfe 11 na dare, amma saboda muna watan Ramadana , kuma yarana sun je sauraron karatu a masalaci, sai muka jira su. Bayan sun dawo gida , mijina ya shigar da yaran cikin gida sai ya fita domin yayi fitsari, kawai sai na gara jin karan harbin bindiga, a take a wurin mijina ya mutu.

An ce mutane da yawa ne suka rasa rayukansu , yan bindigan sunyi hakane domin an kashe musu dan uwa. Kakakin jami'an yan sanda na Jihar,Muyiwa Adejobi, yace yan bindigan kimanin su 100 ne. “ Labari ya iso mana daga wadanda su ke wurin cewa makasa yan bindiga ne kuma daga yankin kudu suke. Duk ba mu tabbatar da haka ba , bincike na gudana. Abin da ya dame mu shine zuwan da suka da yawa.

KU KARANTA: Yaro dan shekara 16 yayi fyade da kisan kai

A wani labari mai kama da wannan, wasu mutanen da ake zargin yan bindiga ne sunyi garkuwa da wani dan sanda mai suna Torbee Atorough na ofishin yan sanda a Ibafo, Jihar Ogun. Jaridar punch ta bada rahoton cewa anyi garkuwa da dan sandan ne a bakin aikin sa a Ibafo.

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel