Takardar jabu: Bani da laifi - Ekweremadu

Takardar jabu: Bani da laifi - Ekweremadu

-Mukaddashin shugaban majalisar dattawa Ike Ekweremadu ya wanke kansa daga zargin yin jabu n ka'idojin majalisa.

Takardar jabu: Bani da laifi - Ekweremadu

Rohotanni daga kahohin watsa labarai na cewa ministan shari'a Abubakar Malami yana kusa da gurfanar da shugaban majalisar da mataimakinsa a kan zargin yin jabun ka'idojin majalisa domin zama shuwagabannin majalisar.

A cikin jawabin da ya rarraba, Ekweremadu, yace hukumar "yan sanda basu taba gayyatarsa ba da sunan ya bada jawabi a kan maganar.

KU KARANTA: Wakilan da suka aikata abun kunya suyi murabus da kujerun su

Jawabin ya cigaba da cewa,

"Kamar sauran "yan kasa, muma abin ya bamu mamaki yadda kwaram sai hukumar "yan Sanda ta mika rohoton ta bayan shekara guda, rohoton da bai ambaci Ekweremadu ba. Haka kuma wadanda suka rubuta takardar korafin basu ambaceni ba"

" yanzu haka ba wata takarda daga "yan sanda, ko kotu wadda ke  neman Mukaddashin shugaban majalisar. Kuma Kowa ya San inda ofis din yake"

"A halin da ake ciki yanzu ba wani abu a kasa, duk dai magana ce ta batanci, cin zarafi da neman firgitar da wadanda ake zargi".

Asali: Legit.ng

Online view pixel