Wakilin pogba ya bayyana yiwuwar zuwan sa Real madrid

Wakilin pogba ya bayyana yiwuwar zuwan sa Real madrid

-Kochi da shugaban Real madrid suna zawarcin dan wasan juventus

-Wakilin paul pogba ya bayyana yiwuwar tafiyar pogban

-manchester united zatayi kokarin dawowa da tsohon dan wasan nata

Wakilin pogba ya bayyana yiwuwar zuwan sa Real madrid
Yan wasan Real madrid

wakilin paul pogba maisuna Mino Raiola, ya tabbatar da cewar real madrid sun fara tattaunawa dashi akan kontaragin dan wasan. Manajan Real madrid ya tabbatar da bukatar sa akan pogba inda yace dan wasan zai dace da kulob din musamman yadda yake wasan sa.

Pogba babban dan wasane, amman muna da yan wasa har guda shida wa'anda sun iya buga tsakiya , amman bazan bayyana yadda al'amarin zai kasance ba acewar Perez.

Da muka juya domin jin ta bakin manajan Real madrid din zidane yace babban dan wasane kuma kungiyoyi zasuso su same shi, amman kuma dan wasa juventus ne kuma yakamata mu girmama hakan: wakilin dan wasan yace daman dan wasan na kyaunar zidane dan haka yasan zidane din zai taka muhimmiyar rawa a cinikin, muna mataki na farko a cinikin tukunna. Pogba yana kyaunar zidane da kuma kungiyar kwallon Real madrid kuma hakan zaiyi tasiri sosai game da hukuncin nasa.

1aiola ya tsaya a €120 million, €140 million? A cewarsa pogba ya chanchanci konawane kulob ta biya a kansa. Haka zalika tsohuwar kulob dinsa manchester united suna zawarcin dan shekaru 23. Rahotanni yanuna manchester sun shirya domin biyan £48m dakuma karin £12m da zasu kara biyan shi idan har dan wasan ya taimaka musu suka taka rawar gani a gasa mai kamawa, wanda kudin da zasu biya yafi kudin da suka biya dan wasan kasar Argentina Angel Di maria wanda suka biyashi zunzurutun kudi har £59.7m kuma yakasa buga mata komai a 2014. Juventus sun saya paul pogba daga manchester united a 2012

Asali: Legit.ng

Online view pixel